An kashe sojoji biyu, an kone gidaje da yawa a sabon harin Jos

An kashe sojoji biyu, an kone gidaje da yawa a sabon harin Jos

Dakarun rundunar sojin Najeriya sun kone gidaje da dama a kudanci da tsakiyar Najeriya sakamakon wasu hare - haren 'yan bindiga da suka yi sanadiyyar mutuwar sojoji shidda (6), kamar yadda majiyar tsaro ta sanar ranar Talata.

Da safiyar ranar Talata ne wasu 'yan bindiga suka harbe dakarun rundunar soji biyu a wata unguwa da ke gefen birnin Jos, mai fama da yawa rikicin kabilanci, kamar yadda wata majiyar 'yan sanda ta sanar da kamfanin dillancin labarai na AFP.

"An kashe sojoji biyu, an raunata guda daya," kakakin rundunar 'yan sandan jihar Filato, Ubah Ogaba, ya sanar.

Bayan kisan sojojin ne sai ragowar sojojin da aka jibge a yankin domin tabbatar da zaman lafiya suka shiga kauyukan Fulani tare da kone gidaje a kalla 150, kamar yadda AFP ta rawaito.

"Sojoji sun kira mu taro, sun fada mana cewa mu fito da masu aikata laifi a cikinmu," a cewar wani mazaunin yankin, Usman Adam.

"Bayan kammala taron ne sai muka ga karin wasu sojoji sun zo yankin, nan da nan kuma suka fara saka wa gidajenmu wuta, nima sun kone gidana," a cewar Adam.

An kashe sojoji biyu, an kone gidaje da yawa a sabon harin Jos
Dakarun soji
Asali: Twitter

Har yanzu rundunar soji basu ce komai ba a kan karin bayanin da kamfanin AFP ya bukata dangane da faruwar lamarin.

Harin na zuwa ne a daidai lokacin da kungiyoyin rajin kare hakkin bil adama ke cigaba da Alla wadai da halayyar wasu sojoji a yankin Neja - Delta mai arzikin man fetur.

DUBA WANNAN: Yawan yi wa miji barazanar kisa da wuka: Kotu ta raba auren mata da miji

A ranar Lahadi ne wasu da ake zargin cewa barayin jirgin ruwa ne suka kai hari a kan wani jirgin dakon danyen man fetur, kammar yadda wata majiya da ta nemi a boye sunanta ta sanar da AFP.

"Yayin harin, 'yan bindigar sun harbe sojoji hudu da farar hula biyu yayin musayar wutar da suka yi," a cewarshaidar.

Sakamakon faruwar hakan ne sai jami'an tsaro suka shiga farautar 'yan bindigar a garin Lutugbene, "inda suka kone gidaje a kalla 21," a cewar, Austin Ozobo, wani jagoran al'umma a garin.

Jami'an tsaron sun tabbatar da cewar sun kai farmaki kauyen tare da bayyana cewa "gidajen da aka kone mallakar 'yan ta'addar da ke kwacen jirgin ruwa ne".

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel