Ran maza ya baci: Hatta jihar Legas akwai Boko Haram - Buratai ya mayar da martani kan harin Boko Haram

Ran maza ya baci: Hatta jihar Legas akwai Boko Haram - Buratai ya mayar da martani kan harin Boko Haram

- Shugaban rundunar sojin Najeriya, Tukur Buratai ya ce babu sassan kasar nan da babu Boko Haram

- Ya shaida cewa an taba bibiyar ‘yan ta’adda har jihar Legas inda aka kama su tare da kulle su

- Buratai ya ce akwai bukatar jama’a su banbance tsakanin ta’addanci da kuma kwace gari gaba daya

Shugaban rundunar sojin Najeriya, Lt.General Tukur Buratai ya ce babu sassan kasar nan da suka fi karfin Boko Haram, har da jihar Legas wacce ake kallo a cibiyar kasuwancin Najeriya kuma jihar da ta kunshi mutane mafi yawa a Najeriya.

A cikin kwanakin nan ne jami’an gwamnatin jihar Legas suka bayyanawa jaridar Pulse cewa an kama wasu mayakan Boko Haram a jihar a watan Disamban da ya gabata. Hakazalika, tsoron kada ‘yan ta’addan su shiga garin na daga cikin dalilin da yasa aka haramta achaba a jihar.

A wata tattaunawa da jaridar ThisDay tayi da shugaban rundunar sojin, ya ce an kama wasu daga cikin mayakan kungiyar a jihar Legas a baya.

“Babu inda ba a samun mayakan Boko Haram, har da jihar Legas kuwa. A jihar Kaduna akwai Boko Haram. Sun dai fi yawa ne a yankin Arewa maso gabas na kasar nan. An kama wasu da yawa kuwa a jihar Legas. Mun bibiyesu ne kuma muka kama su tare da garkamesu,” Buratai ya ce.

KU KARANTA: Mutane biyu sun ga ta kansu yayin da aka kama su lokacin da suka yiwa wata mata karfa-karfa suka kwace mata jariri

Rundunar sojin da kuma fadar shugaban kasar Najeriya na ikirarin cewa an fi karfin ‘yan ta’addan duk da kuwa yawan hare-haren da suke kaiwa yankin Arewa maso gabas din.

Buratai ya ce akwai bukatar jama’a su fara banbance tsakanin kwace gari da kuma ta’addanci. A halin yanzu an fi karfinsu don babu wasu garuruwa da suke hannunsu. Bakin cikin hakan ne kuwa yasa suke fadawa garuruwan yankin su yi kashe-kashe sannan su gudu.

“Mun magance matsalar kwace gari amma muna fama da ta’addanci ne.” cewar Buratai.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel