Mutumin da Ake Zargi da Satar Takalma a Masallaci Ya Fara Girbar Abin da Ya Shuka a Kano

Mutumin da Ake Zargi da Satar Takalma a Masallaci Ya Fara Girbar Abin da Ya Shuka a Kano

  • Kotun Majistare da ke Kano ta bayar da umarnin tsare Muhammad Najib Rimin Kebe a gidan gyaran hali kan zargin satar takalma a masallaci
  • Ana zargin mutumin da kutse da kuma satar takalman masu ibada a masallacin da ke cikin harabar Kotunan Norman’s Land
  • Kotun ta ɗage ci gaba da sauraron shari’ar zuwa ranar 28 ga Agusta, 2026

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Kano, Nigeria - Kotun Majistare da ke Kano ta bayar da umarnin tsare wani mutum mai suna Muhammad Najib Rimin Kebe a gidan gyaran hali bisa zargin satar takalma a wani masallaci da ke cikin harabar Kotunan Norman’s Land.

‘Yan sanda sun gurfanar da wanda ake zargin a gaban kotun ƙarƙashin jagorancin Mai Shari’a Dayyabu Jamilu Hamza, inda aka gabatar da tuhume-tuhumen da ake masa.

Kara karanta wannan

Sojoji sun sauya taku, an tura zazzafan gargadi ga 'yan ta'adda

Kotu.
Gudumar da alkalai ke amfani da ita a zaman kotuna a Najeriya Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

An gurfanar da barawon takalma a Kano

Daily Trust ta ruwaito cewa a yayin zaman kotun, an umarci Adam Salisu Tarauni da ya karanta wa wanda ake zargin tuhume-tuhumen da ake masa, waɗanda suka shafi kutse cikin harabar masallacin da kuma satar takalman masu ibada.

Bayan an karanta tuhume-tuhumen, kotun ta bayar da umarnin a tsare Muhammad Najib Rimin Kebe a gidan gyaran hali domin ci gaba da bin matakan shari’a.

Daga bisani, Mai Shari’a Dayyabu Jamilu Hamza ya ɗage ci gaba da sauraron shari’ar zuwa ranar 28 ga Agusta, 2026, domin ci gaba da duba batun.

Abubuwan da ake zargin barawon

Tun da farko, an zargi Muhammad Najib da yawan zuwa masallacin da ke cikin harabar Kotunan Norman’s Land, inda ake zargin yana amfani da lokacin da mutane suka shiga masallaci domin yin sallah, ya saci takalmansu.

Rahotanni sun nuna cewa matsalar satar takalma ta dade tana addabar masu zuwa masallacin, musamman a lokutan da ake gudanar da salloli, inda wasu mutane ke gano cewa takalmansu sun ɓace bayan sun fito daga masallacin.

Kara karanta wannan

Yadda Najeriya ta fara shirin kera makamai da motoci masu sulke

Wasu daga cikin masu ƙorafin sun haɗa da ma’aikatan kotu, jami’an ‘yan sanda, ma’aikatan hukumar kula da gidajen gyaran hali da kuma sauran jama’ar da ke zuwa wurin domin gudanar da ayyukansu ko ibada.

Sallah.
Yadda musulmai ke gudanar da sallah a wuraren da ska ware domin ibada Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Kotu ta fara zama kan mutumin

A cewar masu ƙorafin, sun sha fuskantar irin wannan matsala ta ɓacewar takalma a masallacin, lamarin da ya janyo damuwa a tsakanin masu ibada.

Sai dai, zarge-zargen da ake yi wa Muhammad Najib Rimin Kebe ba su zama hukunci a kansa ba, domin har yanzu shari’ar tana kan gaba kuma kotu ce za ta yanke hukunci bayan sauraron dukkan ɓangarorin da abin ya shafa.

Gine-gine 2 sun rufta kan mutane a Kano

A wani labarin, kun ji cewa mutane biyar, ciki har da leburori huɗu da ɗalibin makarantar Islamiyya, sun mutu a wasu gine-gine biyu da suka ruguje a jihar Kano.

Hatsarin ruftawar gine-ginen ya faru ne ranar Asabar da ta wuce a Gaida da ke ƙaramar hukumar Kumbotso da Kurna da ke ƙaramar hukumar Fagge ta jihar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262