Kungiyar Arewa ta ci karo Gwamnoni game da Dakarun Shege ka fasa

Kungiyar Arewa ta ci karo Gwamnoni game da Dakarun Shege ka fasa

Kungiyar hadaka da ‘Yan Arewa, CNG, ta samu matsala da gwamnonin yankin kasar a dalilin kafa wasu Dakaru da aka yi na Shege ka fasa domin inganta sha’anin tsaro.

Kungiyar CNG ta fito ta yi magana ne bayan shugaban gwamnonin Arewacin Najeriya, Simon Lalong, ya bayyana cewa gwamnoni ba su cikin wannan shiri da aka kawo.

A Ranar Laraba ne kungiyar CNG ta kaddamar da Dakarun Operation shege ka fasa inda har aka fitar da logonsu. Sai dai an yi wannan ne ba da ilmin gwamnonin Arewa ba.

CNG ta bayyana cewa da gan-gan ta ki sanar da gwamnoni game da wannan tsari, a cewarta, da ace ta sa wani gwamna a cikin maganar, da tuni yanzu an yi watsi da batun.

An kafa Operation Shege ka fasa ne bayan gwamnonin Kudu maso Yamma sun kirkiro Amotekun. Ana sa ran cewa Rundunonin za su yi maganin ta’adin da ake yi.

KU KARANTA: ‘Yan Najeriya su na ganin haza a yau – Inji Sarkin Musulmi

Kungiyar Arewa ta ci karo Gwamnoni game da Dakarun Shege ka fasa
Sarkin Musulmi ya soki kafa Dakarun Shege ka fasa
Asali: UGC

Lalong ya ke cewa: “A game da tambayar da wani ‘Dan jarida ya jefa mani a Jos, ban da wata masaniya game da shirin, a bakin ilmi na, haka duk gwamnonin Arewa."

Kakakin kungiyar CNG, AbdulAzeez Suleiman, shi ne ya shaida wannan a wata hira ‘Yan jarida su ka yi da shi, ya na sukar irin rashin hadin-kan shugabannin Yankin Arewa.

A cewar CNG, babu alamun da ke nuna cewa gwamnonin su na tare da Talakawansu, Suleiman ya yi kira ga shugabanni su dauki darasi da abin da ya faru da Sarkin Potiskum.

Wannan kungiya ta ‘Yan Arewa, ta kuma caccaki Mai martaba Sarkin Musulmi, Mai Alfarma Alhaji Sa’ad Abubakar III da gwamnan jihar Kano na kin goyon bayan tsarin.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel