Babangida: Dole sai kowa ya tashi tsaye wajen ganin bayan Boko Haram

Babangida: Dole sai kowa ya tashi tsaye wajen ganin bayan Boko Haram

Tsohon shugaban Najeriya, Ibrahim Badamasi Babangida, ya yi hira da Jaridar Daily Trust a karshen makon nan, inda ya tabo batutuwa wanda su ka shafi harkar tsaro.

A na sa shawarar, Janar Ibrahim Badamasi Babangida, ya bayyana cewa ya kamata gwamnati ta dage wajen samun bayanan sirri game da yadda ‘yan Boko Haram su ke aiki.

Haka zalika tsohon Sojan Najeriyar ya nuna cewa akwai bukatar Sojojin Najeriya su san wanene manyan shugabannnin Boko Haram da kuma inda su ke samun horaswa.

Ibrahim Babangida ya bayyana cewa Mayakan Boko Haram tsirarrun ‘Yan ta’adda ne kuma ba Sojojin yaki ba ne don haka su ke kokarin jefa tsoro a cikin zukatan ‘Yan kasa.

Bayan haka, tsohon shugaban kasar ya ce akwai bukatar a rika fadakar da jama’a tare da jan hankalinsu game ta’adin ‘Yan kungiyar, IBB ya ce wannan yaki na kowa ne.

KU KARANTA: Shugaban Boko Haram ya na yi wa Pantami, Bukarti barazana

Babangida: Dole sai kowa ya tashi tsaye wajen ganin bayan Boko Haram
Yakin Boko Haram aikin Sojoji ne da farar hula inji Babangida
Asali: UGC

IBB wanda ya mulki Najeriya daga 1985 zuwa 1992 ya bayyana cewa dole sai kowa(Soja da farar hula) ya taka irin na sa rawar ganin wajen kawo karshen rigimar Boko Haram.

Janar Babangida ya bayyana cewa an dade ana samun rigingimu a Najeriya tun farkon kafuwar kasar. Sai dai tashin hankali ya yi kamari ne daga bayan zuwa Soji zuwa yanzu.

A cewar Babangida, bayan yakin basasa a farkon shekarun 1970s, an yi ta fama da matsalar fashi da makami, amma da gwamnati ta tsaya tsayin-daka, sai da aka magance matsalar.

A hirar da ya yi da Daily Trust, tsohon shugaban kasar ya koka da yadda Dajin Sambisar da aka rika horas da Sojojin Najeriya a baya, ya koma hannun ‘Yan ta’addan Boko Haram.

A game da Dakarun Amotekun, Babangida ya nuna cewa akwai alamun cewa aiki ya yi wa Sojoji yawa. IBB kuma ya ce a lokacinsa, Hafsun Sojoji su na da wa'adin shekaru hudu ne,

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel