Buratai ya yi ma Sojoji 3 karin girma saboda jarumta da suka nuna a yaki da Boko Haram

Buratai ya yi ma Sojoji 3 karin girma saboda jarumta da suka nuna a yaki da Boko Haram

Babban hafsan Sojan kasa, Laftanar Janar Tukur Yusuf Buratai ya yi ma wasu dakarun rundunar Sojan Najeriya dake aiki a karkashin rundunar tabbatar da tsaro a yankin Arewa maso gabas, Operation Lafiya Dole karin girma zuwa mukami na gaba.

Daily Trust ta ruwaito Buratai ya yi ma wadannan Sojoji karin girma ne bisa gagarumar gudunmuwar da suke bayarwa wajen yaki da ta’addanci, ta hanyar jarumtar da suke nunawa a fagen daga yayin arangama da mayakan Boko Haram.

KU KARANTA: An yi ba ta kashi tsakanin Sojoji da mayakan Boko Haram a garin Maiduguri

Buratai ya yi ma Sojoji 3 karin girma saboda jarumta da suka nuna a yaki da Boko Haram
Buratai da Sojojin da kwamandansu
Asali: Facebook

Buratai ya yi musu karin girmar ne yayin wata ziyara da ya kai sansaninsu dake jahar Borno a ranar Lahadi, 16 ga watan Feburairu, wannan na daga cikin zayarar da yake kai ma Sojoji a fagen fama domin basu kwarin gwiwa.

Sojojin uku suna aiki ne a sansanin Soji na musamman dake garin Buratai a karamar hukumar Biu, kuma an bayyana sunayensu kamar haka, Warrant Officer Felix Ugwu, wanda aka kara masa girma zuwa Master Warrant Officer.

Sauran kuma sun hada da Corporal Kehinde Goban wanda aka kara masa girma zuwa Sergeant, yayin da Private Ishaq Yusif kuma aka kara masa girma zuwa Lance Corporal, haka zalika Buratai ya baiwa kowannensu kyautan na’aurar samar da wutar lantarki Janareta da katafaren talabijin na bango, Plasma.

Kwamandan sansanin, Kanal Muhammad Adamu ne ya gabatar da Sojoji ga Buratai domin samun lambobin girmamawa kamar yadda Buratai ya bayyana, inda yace kwamandan da kansa ya nemi a kara musu girma saboda gwarzantaka da suke nunawa a fagen yaki.

Don haka ya yi kira ga sauran abokan aikinsu da su yi koyi dasu, kuma su cigaba da aiki tukuru tare da ladabi da biyayya, sa’annan ya tabbatar musu da cewa duk wanda ya cancanci samun karin girma zai ba shi.

A wani labarin kuma, rundunar Sojan sama ta Najeriya ta bayyana rahoton dake yawo a kafafen sadarwa na cewa wai dakarunta sun kashe mayakan kungiyar ta’addanci na Boko Haram guda 250, a matsayin labarun kanzon kurege.

Wannan labari ya fara yawo a kafafen sadarwa ne tun a ranar 13 ga watan Feburairu, kuma wai ya fito ne daga wajen wani mutumi mai suna ‘Comr Aminu Shuaibu Musawa, kamar yadda hukumar sojan sama ta bayyana.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel