Sarkin Kano Muhammad Sanusi Ii
Za ku ji cewa wata Kungiya mai suna Mai Dattaku Network for Empowerment and Development ta ba mata 32 horaswar sana’a inda ta sa mata marasa karfi farin ciki bayan ta tallafa masu da sana'an zamani.
A cewar Ibrahim, za a shafe tsawon kwanaki shidda ana gudanar da tantancewar domin tabbatar da cewa an bayar da dama ga dukkan matasa, maza da mata, da suka nuna sha'awar cin moriyar shirin daga fadin kananan hukumomin jihar Kano
Shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Juma’a, 23 ga watan Agusta ya gana da sarakunan gargajiya daga yankin Arewacin kasar. An fara ganawan ne da misalin karfe 11:30 na safe a majalisar Fadar Shugaban kasa.
Wani bidiyo da yake yawo a shafukan sadarwa ya nuna wani bawan Allah wanda bai bayyana sunansa ba yana bayani akan yadda rikicin gida ya hado su da tsohon shugaban hukumar 'yan sanda na kasa Alhaji Hafiz Abubakar Ringim, inda...
Mun samu wasu tsofaffin hotunan Sarkin Kano da Maidakinsa ta farko a 1980s lokacin su na soyewa. Da alamu Muhammadu Sanusi II da Uwargidansa ta yau sun halarci wani taro ne lokacin a Legas.
A jiya Alhamis ne 15 ga watan Agustan nan, masarautar Kano, karkashin jagorancin Sarki Muhammad Sunusi na biyu ta gabatar da hawan babbar sallah na karshe a wannan shekarar, wanda ake kira da hawan Dorayi...
Gwamnan jihar Kano Dr. Abdullahi Umar Ganduje, ya ce gwamnatinsa ba za ta amince da barna da gangan ba, wanda zai dagula tsarin sabbin masarautun da aka kafa da niyyar samar da cigaba a jihar.
Za ku ga hoton Matan Sarkin Kano hudu. Sa’adiya Ado Bayero ita ce uwargidan sabon Sarki Kano Sanusi Lamido Sanusi, wanda ya ke da ‘Ya ‘ya irin su Fulani Siddika Sanusi, Shahida Sanusi, da Ashraf Sanusi.
Rahotanni sun kawo cewa a ranar Asabar, 10 ga watan Agusta wanda ya kasance jajibarin Sallah , ne Sarkin Gaya, Ibrahim Abdulƙadir ya dakatar da wasu Hakimai saboda sun ki masa biyayya.
Sarkin Kano Muhammad Sanusi Ii
Samu kari