Bayan Kin Bayar da Hakuri, Davido Ya Yi Barazana ga Gwamnan APC

Bayan Kin Bayar da Hakuri, Davido Ya Yi Barazana ga Gwamnan APC

  • Davido ya ce ba zai ba Gwamnan Edo, Monday Okpebholo, hakuri ba kan wallafa sakamakon jarabawar WAEC da ake zargin na gwamnan ne
  • Mawakin ya ce bai yi wani laifi ba, illa sanar da mutanen Edo sakamakon karatun gwamnan nasu
  • Davido ya kuma caccaki Okpebholo kan sukar da ya yi wa kawunsa, Ademola Adeleke, yana mai cewa gwamnan ya bar jiharsa ya zo Osun yana yi masa shagube

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Osun - Fitaccen mawakin Afrobeats, David Adeleke, wanda aka fi sani da Davido, ya ce ba zai ba Gwamnan Jihar Edo, Monday Okpebholo, hakuri ba kan wallafa sakamakon jarabawar WAEC da ake zargin na gwamnan ne.

Davido ya ce bai aikata wani abu mara kyau ba wajen wallafa sakamakon, yana mai cewa kawai ya sanar da mutanen Jihar Edo ne game da tarihin karatun gwamnan nasu.

Kara karanta wannan

"Jama'a sun waye": Jigo a APC ya hango abin da zai sanya Tinubu ya fadi a 2027

Davido ya yi magana kan Okpebholo
Shahararren mawakin Afrobeats, Davido Hoto: Davido
Source: Facebook

Mawakin ya bayyana hakan ne a wata tattaunawa ta musamman da tashar News Central ta yi da shi ranar Talata, 18 ga watan Agustan 2026 a Jihar Osun.

“Ba zan ba da hakuri ba. Ban yi wani abu mara kyau ba. Ina sanar da mutanen jihar ne kawai sakamakon da gwamnan nasu ya samu.”

Abin da ya jawo rikicin

Rikicin ya fara ne bayan Okpebholo ya soki Gwamnan Jihar Osun, Ademola Adeleke, a yayin yakin neman zabe gabanin zaben gwamnan jihar da aka gudanar ranar 15 ga Agustan 2026.

Okpebholo ya yi wa Adeleke ba’a kan yadda yake yawan rawa, yana mai tambayar salon shugabancinsa a yayin da yake yakin neman zaben dan takarar jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a zaben gwamnan jihar, Bola Oyebamiji, wanda aka fi sani da AMBO.

Da yake mayar da martani kan kiran da ake yi masa ya ba gwamnan Edo hakuri, Davido ya kare matakinsa, yana zargin Okpebholo da barin Jihar Edo zuwa Osun domin sukar kawunsa.

Kara karanta wannan

Bayan shan kashi a Osun, shugaban matasan APC ya ba jam'iyyar mafita kan zaben 2027

“Eh, ka zo ka bar jiharka ka zo wata jiha. Ka shigo sannan ka fara cewa kawuna dan rawa ne, ba shi da muhimmanci."
“Har yanzu ba a kammala hanyar zuwa gidan gwamnatin ka ba. Kawuna ba shi da muhimmanci. Da farko ma, ba a zabe ka ba; an zabo ka ne.” In ji shi.

Davido ya soki Okpebholo

Mawakin ya kuma tambayi fahimtar Okpebholo game da abin da ake nufi da samun nasara a zabe.

“Ba ka san abin da ake nufi da lashe zabe ba. Shi ya sa ka iya zuwa can kana magana.” In ji shi.

Davido ya kuma caccaki gwamnan kan sukar da ya yi wa Adeleke, yana mai cewa ya ji tausayin ‘ya’yan Okpebholo.

Davido ya ce ba zai ba Okpebholo hakuri ba
Gwamnan jihar Edo, Monday Okpebholo Hoto: Sen. Monday Okpebholo
Source: Facebook

Haka kuma, ya yi wa Okpebholo ba’a kan zama a otel, inda ya ce:

“Gwamna baki daya yana zama a otel, yana yawo kamar…”

Davido ya gargadi gwamnan Edo cewa Adeleke zai mayar da martanin siyasar idan lokacin ya yi.

“A gaskiya, ka kammala shekaru uku naka, za mu zo mu ziyarce ka idan lokacin sake tsayawa takarar zabe ya yi.” In ji shi.

Kara karanta wannan

Mutane fiye da 10 da Adeleke ya tara wuri daya ya yi masu duka a zaben Osun

Faleke ya yi wa Davido martani

A wani labarin kuma, kun ji ceqa Dan majalisar tarayya mai wakiltar mazabar Ikeja a Legas, James Faleke, ya yi wa Davido martani kan zaben gwamnan Osun.

James Faleke ya musanta zargin yunkurin yin tasiri kan Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) domin sauya sakamakon zaben gwamnan jihar Osun.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng