NDC: Jam'iyyar Su Kwankwaso Ta Zo da Salo bayan INEC Ta Amince a Fara Kamfen
- NDC ta ce za ta bi dabarun da suka dace wajen yakin neman zaben 2027, maimakon fara manyan gangamin siyasa da aka saba gani ana yi
- Jam’iyyar ta ce za ta yi amfani da lokacin da ya rage wajen tsara yakin neman zabe mai tasiri da kuma tuntubar masu ruwa da tsaki
- NDC ta kuma yi Allah-wadai da karin kudin tallan allunan siyasa da wasu gwamnatocin jihohi suka yi, tana cewa hakan na takura wa ’yanci
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja - Jam’iyyar NDC ta ce za ta fitar da dabaru wajen yakin neman zaben 2027, maimakon ta yi gaggawar fara cikakken yakin neman zabe bayan amincewa da a fara kamfen daga yau.
Jam’iyyar ta ce fara wa’adin yakin neman zabe ba yana nufin dole ne ta fara shirya manyan gangami, taruka da sauran ayyukan yakin neman zabe nan take ba.

Source: Twitter
The Nation ta ruwaito cewa NDC ta bayyana cewa za ta yi amfani da albarkatunta cikin tsari tare da tuntubar masu ruwa da tsaki kafin zaben shugaban kasa.
Shiru NDC na fara kamfen
Politics Nigeria ta wallafa cewa Sakataren yada labaran jam’iyyar NDC na kasa, Osa Director, ne ya bayyana hakan yayin da yake magana kan shirye-shiryen jam’iyyar na zaben 2027.
Director ya ce NDC a shirye take ta gudanar da yakin neman zabe mai inganci da tasiri, wanda aka gina bisa tuntubar masu ruwa da tsaki, amma ya bayyana cewa saura kusan watanni biyar kafin zaben shugaban kasa.
Ya ce jam’iyyar za ta yi amfani da lokacin da take da shi wajen samar da dabarun yakin neman zabe da za su isar da sakonta ga ’yan Najeriya yadda ya kamata, maimakon yin gaggawa saboda kawai an dage haramcin yakin neman zabe.
A kalamansa:
“Zaben shugaban kasa ya rage saura kusan watanni biyar. Don haka, muna bukatar mu kasance masu dabara wajen tsara yakin neman zabenmu."
NDC ta yi korafi
Mai magana da yawun NDC ya kuma soki karin kudin amfani da allunan tallan siyasa da wasu gwamnatocin jihohi suka yi, yana gargadin cewa hakan na iya rage damar ’yan siyasa da jam’iyyu wajen isar da sakonsu ga masu kada kuri’a.sss

Source: Facebook
Ya bayyana karin kudin a matsayin abin da bai dace ba, yana cewa ya kamata a bai wa jam’iyyun siyasa damar gudanar da ayyukansu a cikin yanayin da ke kare ’yancin fadin albarkacin baki da kuma yin siyasa cikin adalci.
Director ya ce:
“Muna Allah-wadai da karin kudin allunan talla da wasu jihohi suka yi ba tare da dalili mai ma’ana ba. Wannan ba dimokuradiyya ba ce, kuma yana takaita damar fadin albarkacin baki."
Tsarin NDC kan raba mukamai
A baya, mun kawo labarin cewa Sanata Rabiu Kwankwaso ya bayyana tasirin da kusanci zai yi wajen raba mukaman gwamnati idan yan Najeriya suka zabe shi da Peter Obi.
Kwankwaso ya bayyana cewa kwarewa da cancanta za su fi komai taka rawa a gwamnatin da jam'iyyar NDC ke kokarin kafa wa a Najeriya da zarar yan Najeriya sun zabe ta.
'Dan takarar mataimakin shugaban kasar ya ce gwamnatin NDC za ta yi gaggawar kafa majalisar ministoci domin fara aiki nan take bayan rantsar da ita ba tare da bata lokaci ba.
Asali: Legit.ng


