Sarki mai adalci: Sarki Sunusi yayi abin da babu wani Sarki da ya taba yi a fadin Najeriya

Sarki mai adalci: Sarki Sunusi yayi abin da babu wani Sarki da ya taba yi a fadin Najeriya

- Sarkin Kano Muhammadu Sunusi na biyu yayi wani abu da duk Najeriya babu wani Sarki mai daraja irin tasa da ya taba yi

- Sarkin ya bukaci a sauke masa lema ruwan sama ya jika shi, a lokacin da wani ruwa ya tsinke kamar da bakin kwarya daidai lokacin da ake gudanar da hawan karshe na babbar sallah jiya

- Wannan lamari ya yiwa Hakimai da Dogarawansa dadi matuka, inda kuma aka yi hawan lafiya aka kare lafiya

A jiya Alhamis ne 15 ga watan Agustan nan, masarautar Kano, karkashin jagorancin Sarki Muhammad Sunusi na biyu ta gabatar da hawan babbar sallah na karshe a wannan shekarar, wanda ake kira da hawan Dorayi.

A lokacin da ake gudanar da wannan hawa ne aka barke da wani matsanancin ruwan sama kamar da bakin kwarya. Kowa dai ya san cewa a al'ada Sarki a cikin lema yake yawo a lokacin da ake gabatar da hawan sallah a kasar Hausa.

KU KARANTA: Tashin hankali: Tsananin talauci da yunwa yasa na taba cin kashin mutum - In ji wata mawakiya

Wannan ruwa da ya tsinke ne ya sanya Sarkin ya dubi Hakimansa da Dogarawa yaga duka suna cikin ruwa, kuma basu nuna gajiyawarsy ba, nan take Sarkin ya umarci mai daga lema da ya sauke lemar, saboda shima yaji irin halin da talakawansa suke ji.

Ba musu mai rike da lema ya sauke lemarsa, Sarki ya koma kamar talakawansa shima ruwa yayi masa dukan tsiya.

A tarihi ba a taba samun irin wannan ba kaf Sarakunan yankin arewa dama Najeriya baki daya.

Wannan abu da Sarkin Kanon yayi ya sanya Hakimai da Dogarawansa sunji dadi kwarai da gaske, an kuma gabatar da hawan Sallar lafiya an kuma kare shi lafiya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel