Sabbin masarautu: Ganduje ya aika sakon gargadi ga sarakuna, yace ba zai lamunci barna da gangan ba

Sabbin masarautu: Ganduje ya aika sakon gargadi ga sarakuna, yace ba zai lamunci barna da gangan ba

Gwamnan jihar Kano Dr. Abdullahi Umar Ganduje, ya ce gwamnatinsa ba za ta amince da barna da gangan ba, wanda zai dagula tsarin sabbin masarautun da aka kafa da niyyar samar da cigaba a jihar.

Ganduje ya bayyana hakan ne yayin da yake jawabi ga dubban mutane daga kananan hukumomin da ke karkashin masarautan Karaye, a lokacin hawan Kutifi wanda masarautar ta shirya a bikin babban Sallah na shekarar nan.

Da ya samu wakilcin mataimakin gwamna, Dr. Nasiru Yusuf Gawuna, Ganduje yace gwamnatin jihar Kano ta kammala shirye-shirye wajen gina babban asibiti mai daukar gadaje 400 a kowace masarauta.

Ya kara da cewa akwai shirye-shirye don gudanar da ayyuka a masarautun guda biyar domin amfanin al’ummansu.

Dr. Ganduje yace an kafa sabbin masarautun ne don kawo cigaba ga tattalin arziki da rayuwar mutanen jihar, inda ya bayyana cewa an samu sauye-sauye da kuma cigaba a fannin hadin kai da cig aba tsakanin yankunan kananan hukumomi a jihar.

A jawabinsa, Sarkin Karaye, Dr Ibrahim Abubakar II yayi addu’a akan cigaba da zaman lafiya da daidaituwa a Kano da kuma kasar baki daya.

KU KARANTA KUMA: Sarkin Kano Sanusi II ya sake samun wani mukami daga kasar waje

A baya dai Legit.ng ta rahoto cewa wasu hakimai 11 da suka fada arkashin sabbin masarautun da gwamnan jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya kirkira sun halarci hawan Sallah na yammacin ranar Litinin a masarautar sarkin birnin Kano, Mai Martaba Sarki Muhammadu Sanusi II.

Sun halarci hawan na 'Daushe' ne sabanin umarnin da gwamnatin Kano ta fitar a kan cewa kowanne hakimi ya halarci hawa Sallah a karkashin sabon sarkin masarautarsa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel