Yanzu Yanzu: Buhari na cikin ganawa da sarakunan arewa a Abuja

Yanzu Yanzu: Buhari na cikin ganawa da sarakunan arewa a Abuja

Shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Juma’a, 23 ga watan Agusta ya gana da sarakunan gargajiya daga yankin Arewacin kasar.

An fara ganawan ne da misalin karfe 11:30 na safe a majalisar Fadar Shugaban kasa.

Daga cikin wadanda suka halarci taron akwai Sarkin Musulmi kuma Sultan na Sokoto, Alhaji Abubakar Sa’ad; Sarkin Kano, Muhammad Sanusi Lamido, Sarkin Bida, Etsu Yahaya Abubakar da kuma Sarkin Daura.

Har yanzu ana kan gudanar da taron a daidai lokacin kawo wannan rahoton.

Ga hotunan haduwarsu a kasa:

Yanzu Yanzu: Buhari na cikin ganawa da sarakunan arewa a Abuja
Shugaba Buhari tare da sarakunan arewa a Abuja
Asali: Twitter

Yanzu Yanzu: Buhari na cikin ganawa da sarakunan arewa a Abuja
Buhari ya ganawa da sarakunan arewa a Abuja
Asali: Twitter

Yanzu Yanzu: Buhari na cikin ganawa da sarakunan arewa a Abuja
Buhari tare da Sarki Sanusi
Asali: Twitter

KU KARANTA KUMA: Babban magana: Magoya bayan Uche Nwosu sun lakada wa jami’an DSS dukan tsiya

A wani labarin kuma, Legit.ng ta rahoto a baya cewa Gwamnatin tarayya da gamayyar kungiyar ‘yan kwadago za su zauna domin kai karshe a kan maganar mafi karancin albashin ma’aikata ranar Juma’a 23 ga Agusta.

Jaridar The Nation ta ruwaito cewa ana sa ran za a cinma matsaya guda wadda kuma za ta kasance ta karshe bayan wannan ganawar.

Ministan kwadago Sanata Chris Ngige ya shaidawa manema labarai a ranar Laraba cewa maganar mafi karancin albashi ita ce kan gaba a cikin ayyukan da zai soma yi da zarar ya shiga ofis.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel