An kantarawa Naziru Sarkin Waka karya ta ban mamaki da ta sanya shi nuna fushin sa

An kantarawa Naziru Sarkin Waka karya ta ban mamaki da ta sanya shi nuna fushin sa

- Wasu labaran bogi da suke ta yawo a shafukan sada zumunta sun tunzura mawaki Nazir Ahmad

- An wallafa labaran ne inda aka yiwa mawakin kagen cewa ya ce zai tonawa kungiyar Kwankwasiyya asiri

- Mawakin ya ce shi kwata-kwata bai san da wannan labari ba, kuma yana yiwa mutanen da suke yada irin wannan labari addu'ar Allah yasa suji tsoron Allah su daina

A jiya aka fara yada wani marar tushe game da fasihin mawakin Sarautar nan Nazir Ahmad Sarkin Wakan San Kano, akan 'yar hatsaniyar da ta faru tsakanin magoya bayan Kwankwasiyya da Sheikh Isah Ali Fantami.

Ko da yake an san cewa akwai kyakkyawar alaka tsakanin mawakin da malamin domin kuwa an sha ganin hotunan su tare kuma har waka ma yayi masa, amma ko da ake tsaka da cece kuce kan wannan lamarin, har yanzu ba aji koda kalma daya daga bakin mawakin ba hana rantsuwa ya wallafa jawabin jarumi Nabraska inda ya nuna goyon bayan sa da jawabinsa da yake nuna rashin jin dadin su akan abin da aka yiwa malamin.

KU KARANTA: Anyi barazanar kashe Mansurah Isah matukar bata tura zunzurutun kudi har dalar Amurka dubu daya da dari biyar ba

Ana haka kuma kwatsam sai wannan rahoton na karya ya bayyana inda aka wallafa cewa:

"Zan tona asirin Kwankwasiyya - Naziru Sarkin Waka, daga jaridar Sarauniya.

"Wani rahoto da mu ka samu daga majiya mai karfi, an jiyo sarkin wakar Sarkin Kano Naziru M Ahmad ya na ikirarin fasa kwan kungiyar Kwankwasiyya muddin dai ba su daina zaginsa ba.

"A saboda na goyi bayan Malam Isah Ali Pantami wai yau ni Naziru Sarkin Waka 'yan Kwankwasiyya za su rika zagi da furta kalaman batanci da yarfe da kuma kage a kaina."

Bayan bayyanar wadannan labarai, Nazir ya kwafo shafukan da suka wallafa wadannan labarai gami da wallafawa a shafinsa na Instagram sannan ya karyata su ya kuma tabbatar musu da cewa babu kyau su ji tsoron Allah su daina yada labaran da basu da tushe.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel