Sarkin Kano ya ba Surajo Labbo sarautar Sarkin Hausawa a Turai

Sarkin Kano ya ba Surajo Labbo sarautar Sarkin Hausawa a Turai

Mun samu labari daga Daily Nigerian cewa Sarkin Birnin Kano Muhammadu Sanusi II ya ba Dr. Surajo Jankado Labbo sarauta a matsayin Sarkin Hausawan na kasashen Turai.

Jaridar ta rahoto cewa an yi wannan nadi ne a cikin karshen makon nan inda Surajo Jankado Labbo ya zama Jagoran Hausawan da ke zaune a kaf kasashen Nahiyar Turai.

An yi nadin sarautar ne bayan wani zaman fada da sarkin ya yi a babban Birnin Faris na kasar Faransa. Wannan ne karon farko da Sarkin ya yi zaman fada a kasashen ketare.

Kamar yadda hotuna su ka nuna, an kawata fadar Sarkin da kayan ado da alatu na gargajiya da tarihi wajen wannan zama da bikin nadin sarauta da aka yi wa Dr. Surajo Labbo.

KU KARANTA: Sarki Muhammadu Sanusi II tare da Mai dakinsa a shekarun baya

Manyan wadanda su ka halarci wannan nadi da aka yi wa Surajo Labbo a Ranar 29 ga Satumba sun hada har da gwamnonin Biranen Palaiseau, Gregoire da kuma Lasteyrie.

A daidai lokacin da aka yi wannan biki, Sarkin na Kano ya na fuskantar barazana daga gwamnati inda ake zargin cewa an sake shirya wani kutun-kutun din tsigesa daga gado.

Fitaccen Sarkin ya yi wannan nadin sarauta ne a lokacin da ya kai ziyara zuwa kasashen na ketaren domin halartar babban taron majalisar dinkin Duniya da aka yi a Amurka.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari na Najeriya ya na cikin manyan bakin da aka gayyata wajen wannan taro na majalisar dinkin Duniya da aka yi a babban Birnin New York.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel