Dandazon Kanawa sun yi dafifi wajen fito wa tarbar Ganduje

Dandazon Kanawa sun yi dafifi wajen fito wa tarbar Ganduje

Dandazon jama'a a jihar Kano sun yi dafifi wajen fito wa tarbar gwamnan jihar, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, bayan dawowarsa daga rakiyar da ya yi wa shugaban kasa, Muhammadu Buhari, zuwa kasar Afrika ta Kudu.

Ganduje ba ya Najeriya a lokacin da alkaliyar kotun sauraron korafin zaben gwamnan jihar Kano, Jastis Halima Shamaki, ta zartar da hukuncin tabbatar masa da nasarar da ya samu a zaben gwamnan jihar da aka yi a watan Maris, wanda kuma hakan ne yasa jama'a yin dandazo wajen taryarsa.

Gwamna Ganduje ya sauka a filin tashi da saukar jirage na Malam Aminu Kano (MAKIA) da misalin karfe 1:30 na rana. A cikin jirgin kamfanin 'Max Air' Ganduje ya dawo Kano daga Abuja.

Ganduje, wanda ya samu tarbar dubban masoyansa da magoya bayan jam'iyyar APC, ya bi ta wasu zababbun hanyoyi yayin da yake koma wa gidan gwamnatin jihar Kano.

Jerin gwanon ababen hawa da masu tarbar gwamnan sun bi ta Kofar Ruwa, Gwammaja, Cikin Gari, da Kofar Nasarawa kafin daga bisani su wuce zuwa gidan gwamnati.

DUBA WANNAN: Buhari ya gana da ministocinsa a lokacin mulkin soja daga 1984 zuwa 1985 (Hotuna)

Tafiyar da zata kai Ganduje gidan gwamnati daga MAKIA bata wuce minti 15, amma ta dauke shi fiye da sa'a guda saboda yawan jama'a da cunkuson ababen hawa.

Jaridar Daily Trust ta rawaito cewa fitowar dubban masu tarar gwamnan ya haddasa cunkuson ababen hawa a cikin birnin Kano, musamman hanyoyin da gwamnan ya bi.

Tsananin zafin rana bai hana wasu masoya da goyon bayan gwamnan da basu samu wuri a ababen hawa ba, yin tattaki tun daga MAKIA har zuwa gidan gwamnatin jihar Kano don nuna murnarsu da nasarar da Ganduje ya samu a kotu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel