Wike Zai Rugurguza Wasu Gidajen da Sanatoci da Manya Suka Gina a Abuja

Wike Zai Rugurguza Wasu Gidajen da Sanatoci da Manya Suka Gina a Abuja

  • Ministan harkokin Abuja, Nyesom Wike ya ba da umarnin rushe dukkan gidajen da ke kan hanyoyin ruwa
  • Ya ja kunnen sanatoci da manyan mutane kan cewa ba za a saurare su ba idan gidajensu sun tare hanya
  • Bisa umarnin na Wike, ma'aikatar gudanar da birnin tana da daga yanzu zuwa Asabar domin ruguza gine-ginen

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada

FCT, Abuja - Ministan harkokin birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike ya bada umarnin rusa gidajen da suka tare hanyoyin ruwa.

Mahukuntan birnin Abuja za su ruguza gidajen da aka gina a kan hanyoyin ruwa a Maitama da wasu unguwanni da za a iya ambaliya.

Wike.
Ministan harkokin birnin tarayya, Nyesom Wike lokacin duba gyaran da ruwa ya yi a Abuja Hoto: @OlayinkaLere
Source: Twitter

Za a rusa gidajen da ke hanyar ruwa

Nyesom Wike ya bada umarnin ne ranar Talata da ya ziyarci inda ambaliya ta shafa a Maitaima a cewar rahoton da The Cable ta fitar.

Kara karanta wannan

Cutar Apollo ta ɓarke a wasu jihohin Arewacin Najeriya, ta fara yaɗuwa cikin jama'a

Ministan ya ce za a fara rushe-rushen ne ba tare da wani bata lokaci ba kuma za a cigaba har zuwa ranar Asabar dinnan mai zuwa.

Mai girma ministan ya kuma bayyana cewa za a ruguza gine-ginen jama’a ba tare da la’akari da akidar siyasa ko matsayin masu su ba.

Ganin yadda ambaliyar ruwa ta yi wa wasu wurare, ministan ya tabbatar da cewa ba za a cigaba da kallon masu saba wa dokokin gini ba.

Ko me zai faru sai an kai gine-ginen kasa

Duk wani gini da aka samu a kan hanyar wucewar ruwa da ke kan tsarin ginin Abuja, za a rushe shi ko da ya dade a tsaye a birnin Abuja.

Ana ganin wannan mataki zai iya taba gwamnati musamman ganin zabe ya gabato, amma tsohon gwamnan ya ce babu ruwan shi da hakan.

"Za mu rushe duka gidajen da aka samu kan hanyar ruwa. Wasu gidajen sanatoci ne. Wasunsu manyan mutane ne.

Kara karanta wannan

Yadda motoci suka nutse, komai ya tsaya cak bayan ambaliya a Abuja

"Ko akwai zabe ko babu zabe, za a kai duka gidajen nan kasa. Ko sama da kasa za su hade. Sai dai ma a fi da zaman lafiya domin an yi abin da ya dace.”

- Nyesom Wike

Babu ruwan Wike da tasiri ko siyasar masu ginin

Daily Trust ta rahoto shi yana cewa matsayi ko akidar siyasar masu gidajen ba za su yi tasiri ba wajen ganin an yi waje da gine-ginen.

Ministan yana da ra’ayin cewa abubuwan da mutane suke yi ne ya jawo aka samu ambaliyar ruwa kwana nan a wasu unguwannin Abuja.

Wike ya zargi jama’a da toshe magudanun ruwa, jefar da bola kan hanya da kuma rashin gyaran kwatoci da ruwa zai wuce salin-alin.

An bukaci mahukunta su kuma fara gyaran lambatu domin maganace matsalar da aka fuskanta a yanzu da aka samu karuwar ruwan sama.

Hadimin ministan, Olayinka Lere ya fitar da jawabi na musamman a shafin X.

Garuruwan da za a sharba ruwan sama

Ana da labari NiMet ta yi hasashen samun tsawa da ruwan sama a sassa daban-daban na jihohin Arewa, Arewa ta Tsakiya, da Kudancin Najeriya.

Kara karanta wannan

Miji ya sakawa matarsa fetur, ya banka mata wuta ta kone

Ana sa ran ruwan saman zai ƙaru daga rana zuwa yamma, tare da matsakaicin ruwa a jihohi irin su Kano, Gombe, Katsina, da kuma birnin Abuja.

NiMet ta gargadi jama'a, musamman masu zama a wuraren da ambaliya ke yawan faruwa da masu abubuwan hawa, da su kasance cikin shiri tun wuri.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng