Kungiyar Mai Dattaku ta ba mata 32 horaswar sana’a a Kano

Kungiyar Mai Dattaku ta ba mata 32 horaswar sana’a a Kano

Wata kungiya mai zaman kan ta a Najeriya mai suna “Mai Dattaku Network for Empowerment and Development” ta dafawa wasu mata da hanyoyin samun na kan su a Arewacin Najeriya.

Kamar yadda mu ka samu labari, wannan kungiya da ke aiki a jihar Kano, ta tallafawa mata akalla 32 da dabarun yin kayan yayi na zamani. Wannan zai taimaka kwarai wajen rage rashin aikin yi.

Shugaban wannan kungiya, Malam Umar Farouq Yola, wanda ya shirya wannan tallafi, ya bayyana cewa sun zabi mata 32 daga cikin sama da 60 da su ka nemi samun shiga wannan aiki.

An horas da wadannan mata ne a kan yadda za su rika yin kayan yayi kamar yadda Umar Yola ya bayyana. An yi bikin yaye Matan ne bayan sun kammala koyon aikin a Ranar Asabar da ta gabata.

A wajen wannan gagarumin biki da aka gudanar a Ranar 14 ga Watan Satumba, 2019, Umar Yola, ya bayyana cewa an kashe kudi sama da Naira miliyan uku wajen tallafawa wadannan Mata.

KU KARANTA: Karuwanci: Hukumomin Ghana za su taso keyar ‘Yan matan Najeriya gida

A cewar Malam Yola wanda aka fi sani da Mai Dattaku, an soma horas da wadannan Bayin Allah ne tun a farkon shekarar bana inda su ka karkare koyon aikin bayan kusan watanni bakwai.

Gidauniyar Mai Dattaku ta na sa ran cewa rukuni na biyu na matan da za a ba irin wannan tallafi za su soma samun na su horaswar a watan Oktoban gobe. Zaurawa ne mafi yawan masu amfana.

Mai Dattaku ya bayyana cewa gidauniyar nan ta sa ta samu kudi ne bayan sun nemi gudumuwa kwanakin baya. Matashin ya yi kira ga jama’a su sa hannu wajen ganin maganin talaucin mata.

Wadanda su ka samun wannan tallafi sun nuna matukar farin cikinsu. Shugaban wannan kungiya, shi ma ya yi farin cikin ganin Dattijon Mahaifinsa a wajen taron kamar yadda ya shaida.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel