Bidiyo: Tsohon shugaban hukumar 'yan sanda na kasa Hafiz Ringim yana yi mini barazanar kisa akan hakkina - In ji wani dan Kano

Bidiyo: Tsohon shugaban hukumar 'yan sanda na kasa Hafiz Ringim yana yi mini barazanar kisa akan hakkina - In ji wani dan Kano

- Wani bawan Allah wanda bai bayyana sunanshi ba ya bayyana a wani bidiyo, inda yake bayyana cewa tsohon shugaban hukumar 'yan sanda na yi masa barazanar kisa

- Mutumin ya ce hakan ya biyo bayan shiga hakkinsu da shugaban hukumar 'yan sandan yake kokarin yi akan wani gida da suka gada a wajen mahaifinsu shekaru da dama da suka wuce

- A karshe yayi kira ga gwamnatin jihar Kano da kuma masarautar Kano akan su kawo masa dauki akan wannan lamari, inda ya ce lokacin da yayi masa magana barazanar kisa yake yi masa

Wani bidiyo da yake yawo a shafukan sadarwa ya nuna wani bawan Allah wanda bai bayyana sunansa ba yana bayani akan yadda rikicin gida ya hado su da tsohon shugaban hukumar 'yan sanda na kasa Alhaji Hafiz Abubakar Ringim, inda har ta kai ga yana yi masa barazanar kisa.

Mutumin ya bayyana cewa sun fara rigimar akan filin ne da Hafiz Ringim bayan yayi kokarin ya shiga iyakarsu da niyyar yin katanga wacce za ta rufe musu kofar su da suke shiga da fita daga gidan su.

Ya ce wannan gida nasu dai guda biyu ne suka gajeshi a wajen mahaifinsu wanda Allah yayi masa cikawa, daga baya kuma sai Hafiz Ringim ya siyi gida daya a hannun Kawunsu, bayan ya siya ne kuma ya tada katanga wacce ta shigo daga gidansu za ta rufe musu kofar gida.

KU KARANTA: Tashin hankali: Bidiyon yadda Baban Chinedu ya dinga tona asirin babban abokinshi Rarara

Mutumin ya kara da cewa idan har tsohon shugaban 'yan sandan ya gina wannan katangar to sanadiyyar ta ruwa zai iya cinye gidansu

Ya bayyana cewa da suka yi masa korafi akan wannan lamari, sai ya zo har gidansu da 'yan sanda ya zazzage su ya ci musu mutunci, inda har ya dinga yi musu barazanar kisa ko kuma ya saka a daure su idan basu yi shiru da bakinsu ba.

Mutumin ya ce yana rokon gwamnatin jihar Kano karkashin jagorancin gwamnan jihar Alhaji Abdullahi Umar Ganduje, da kuma Sarkin Kano Muhammadu Sanusi na biyu da su kawo musu dauki akan wannan lamari, ya kara da cewa lokacin da yayi masa magana akan wannan shiga hakki nasuda yake kokarin yi ya turo yaransa ne inda suka ce za su kashe shi, inda ya kara da cewa wannan abu ya faru akan idon mutane sama da ashirin.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel