Bayar da tallafi: FG ta fara tantance masu bukata ta musamman a Kano

Bayar da tallafi: FG ta fara tantance masu bukata ta musamman a Kano

Ofishin bayar da tallafin harkar noma, APPEAL (Agro Processing Productivity Ehancement and Livelihood Support), reshen jihar Kano ya fara tantance mutane 303 masu bukata ta musamman, da suka nuna sha'awar cin moriyar shirin.

Kamfanin dillancin kabarai na kasa (NAN) ya rawaito cewa gwamnatin tarayya ce tare da hadin gwuiwar gwamnatin jihohi da bankin duniya ke daukan nauyin shiri domin bawa masu bukata ta musamman damar dogaro da kansu.

Da yake magana a wurin tantancewar da za a shafe kwanaki shidda ana yi, Alhaji Hassan Ibrahim, jagoran shirin a jihar Kano, ya ce suna tantancewar ne domin tabbatar da cewa mutanen da ke da bukata ta musamman ne kawai zasu ci moriyar shirin.

Ya kara da cewa bayan an kammala tantancewar, za a gayyaci wadanda suka samu nasara domin a gana da su kafin a fara basu horo da kuma jari a bangarorin sana'o'in harkar noma da suka zaba.

Ibrahim ya bayyana cewa APPEALS zata bayar da tallafi a bangarorin noma guda tara da suka hada da; noman shinkafa, alkama, tumatur, kashu, citta, noman kifi da sauransu.

DUBA WANNAN: An kama matashin da aka kwantar a asibiti da laifin sata, an mayar da shi kurkuku

A cewarsa, a kwanakin baya ne masu bukata ta musamman su 41,000 suka karbi fom daga ofishin APPEALS domin nuna sha'aarsu a kan shirin. Kazalika, ya bayyana cewa an dawo da fom 32,000 da aka kammala cike su.

"An ware wa masu bukata ta musamman kaso 10% na masu cin moriyar shirin, kuma daga cikinsu ne za a dauki wadanda suka cika sharudan da aka saka kafin cin moriyar shirin," a cewarsa.

A cewar Ibrahim, za a shafe tsawon kwanaki shidda ana gudanar da tantancewar domin tabbatar da cewa an bayar da dama ga dukkan matasa, maza da mata, da suka nuna sha'awar cin moriyar shirin daga fadin kananan hukumomin jihar Kano 44.

A jawabinsa, sarkin kutaren Kano, Alhaji Isyaku Mohammed, ya ce shirin zai taimaka wajen rage wahalar da masu bukata ta musamman ke sha wajen ganin sun dogara da kansu tare da yin kira ga wadanda zasu ci moriyar shirin a kan su yi amfani da tallafin ta hanyar da ya dace.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel