Duk da Mamayar APM a Zaɓen Ciyamomi, Wasu Jam'iyyu Sun Samu Kujeru 4 a Bauchi
- Hukumar zaben jihar Bauchi, BASIEC ta gudanar da zabukan ƙananan hukumomi a jiya Litinin domin samar da ciyamomi
- APM ta yi nasara a zaben inda ya lashe kujerun kansiloli 319 cikin 323, yayin da SDP, NRM, ZLP da YPP suka samu kujera daya kowannensu
- Shugaban BASIEC, Hajiya Jummai Abubakar, ta tabbatar da sakamakon, tana mai cewa an gudanar da zaben bisa doka da kuma ka’idojin hukumar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Bauchi - Jam’iyyar APM mai alamar rogo ta yi bajinta bayan sanar da sakamakon zaben kananan hukumomi a Bauchi.
APM ta lashe dukkan kujerun shugabannin kananan hukumomi 20 da kuma kujerun kansiloli 319 cikin 323 a zaben kananan hukumomin Bauchi.

Source: Original
Bauchi: An sanar da sakamakon zaben ciyamomi
Hukumar Zaben Kananan Hukumomin Bauchi (BASIEC) ce ta sanar da sakamakon zaben a daren Litinin, bayan kammala kada kuri’a, kirga kuri’u da tattara sakamako, cewar Tribune.
Hukumar ta ce jam'iyyar APM ta lashe kujerar shugabanci a dukkan kananan hukumomi 20 na jihar, yayin da wasu jam’iyyu hudu suka raba sauran kujerun kansiloli.
Da take bayyana sakamakon, shugabar BASIEC, Hajiya Jummai Abubakar, ta ce ‘yan takarar da suka yi nasara sun samu nasarar ne bayan kammala kada kuri’a, kirga kuri’u, tattarawa da tantance sakamako.
Daga cikin ‘yan takarar APM, Umar Mohammed Aliyu ya samu mafi yawan kuri’u, inda ya lashe Bauchi da kuri’u 125,170.
Abubakar Ibrahim Dembo ya zo na biyu, inda ya samu kuri’u 109,999 a Toro, yayin da Bappah Aliyu Mohammed ya lashe Alkaleri da kuri’u 107,482.
Ya’u Samaila Sade ya lashe zaben Darazo da kuri’u 67,276, yayin da Yusuf Babayo Zaki ya samu nasara a Katagum da kuri’u 65,626.
Sauran wadanda suka yi nasara sun hada da Ali Babayo a Gamawa da kuri’u 54,423; Sama’ila Wakili Lere a Tafawa Balewa da 46,625; da Habibu Idris Usman a Warji da 43,066.

Source: Twitter
Yadda APM ta yi bajinta a Bauchi
A Shira, tsohon Shugaban Masu Rinjaye na Majalisar Dokokin Bauchi, Saleh Hodi Jibir, ya lashe zaben shugabancin karamar hukumar da kuri’u 37,135.
Sauran ‘yan takarar APM da suka yi nasara sun hada da Zakka Luka Magaji a Bogoro da kuri’u 25,282; Iliya Isah a Dambam da 19,730; da Mohammed Abubakar Jibo a Dass da 35,264.
Mohammed Idris M. ya lashe Ganjuwa da kuri’u 24,150, Mustapha Alhaji Musa ya lashe Giade da 33,864, yayin da Dankawuwa Ya’u ya lashe Itas/Gadau da 24,989.
Inuwa Abdullahi ya lashe Jama’are da kuri’u 36,766, Garba Musa ya lashe Kirfi da 24,787, Salisu Hussaini ya samu nasara a Misau da 34,378.
Yahuza Adamu Haruna ya lashe Ningi da kuri’u 29,387, yayin da Mas’ud Aliyu ya lashe Zaki da kuri’u 19,984, cewar Punch.
Nasarar da wasu jam'iyyun adawa suka yi
Duk da mamayar da APM ta yi a zaben kansiloli, jam’iyyu hudu sun samu kujera daya kowannensu a wasu mazabu.
SDP ta lashe yankin Dandango a karamar hukumar Bauchi, yayin da National Rescue Movement (NRM) ta samu nasara a unguwar Darazo ta Kudu.
Jam'iyyar ZLP ta lashe mazabar Wandi a karamar hukumar Dass, yayin da Young Progressive Party (YPP) ta samu nasara a yankin Zirami na karamar hukumar Giade.
Gwamna Bala ya caccki yan adawa a Bauchi
An ji cewa Gwamna Bala Mohammed ya ce jam’iyyun adawa da suka kaurace wa zaben kananan hukumomi a Bauchi matsorata ne saboda tsoron faduwa.
Jam'iyyar APM ta lashe dukkan kujerun shugabannin kananan hukumomi 20 da aka fafata a zaben da aka gudanar.
Hakazalika, jam’iyyar ta kuma lashe kujerun kansiloli 319 daga cikin 323 da aka fafata wajen neman lashe su a jihar.
Asali: Legit.ng


