Gyaran tattalin arziki: Sanusi Lamido ya jinjina wa shugaba Buhari

Gyaran tattalin arziki: Sanusi Lamido ya jinjina wa shugaba Buhari

Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, ya yaba wa shugaban kasa, Muhammadu Buhari, a kan kafa sabon kwamitin da zai ke bashi shawara a kan harkokin da suka shafi tattalin arzikin kasa (EAC).

Da yake magana da manema labarai a fadarsa ranar Laraba, sarki Sanusi ya ce shugaba Buhari ya yi abinda ya dace ta hanyar nada kwararrun masana tattalin arziki, da suka san ciki da wajen tattalin arzikin Najeriya, a cikin sabon kwamitin.

A cewarsa, shugaba Buhari ya dauki matakin da ya dace ta hanyar zabo kwararrun masana tattalin arziki masu basira domin bashi shawarwari a kan gyaran tattalin arzikin kasa a daidai lokacin da tattalin arzikin duniya ke fuskantar barazana saboda adawar kasuwanci a tsakanin wasu manyan kasashe.

Sarki Sanusi ya bayyana mambobin kwamitin a matsayin masu gogewa a bangaren tattalin arziki, tare da bayyana cewa yana da yakinin cewa zasu farfado da tattalin arzikin Najeriya.

DUBA WANNAN: Bill Gates ya yi wa gwamnatin Najeriya gugar zana

Ya kara da cewa saka irin wadannan kwararrun masana a cikin kwamitin, ita ce shawara mafi alheri da gwamnatin Buhari ta yanke.

Basaraken ya ce shugaba Buhari ya cancanci jinjina da goyon baya bisa daukan matakin farfado da tattalin arzikin Najeriya da ya dade a cikin mawuyacin hali, ya kara da cewa babu wasu kwararrun masana tattalin arziki da zasu taimaka wa gwamnati ta cimma nufinta fiye da mutanen da Buhari ya nada a cikin EAC.

Kazalika, sarki Sanusi II ya musanta cewa ya soki manufofin gwamnatin Buhari a kan tattalin arziki, tare da zargin kafafen yada labarai da sauya ma'anar kalamansa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel