Jerin sunayen Hakiman da sarkin Gaya ya dakatar saboda ci gaba da yi wa sarkin Kano mubaya'a

Jerin sunayen Hakiman da sarkin Gaya ya dakatar saboda ci gaba da yi wa sarkin Kano mubaya'a

Rahotanni sun kawo cewa a ranar Asabar, 10 ga watan Agusta wanda ya kasance jajibarin Sallah , ne Sarkin Gaya, Ibrahim Abdulƙadir ya dakatar da wasu Hakimai saboda sun ki masa biyayya.

Hakiman da lamarin ya shafa sun hada da na; Wudil Sarki Ibrahim, Hakimin Gabasawa Bello Abubakar, Hakimin Warawa, Kabiru Hashim, Hakimin Dawakin Kudu, Yusuf Bayero da Hakimin Garko Mohammed Aliyu.

Wadannan Hakiman dai na daga cikin wadanda suka ci gaba da yi wa sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II biyayya duk da sabbin masarautun da Gwamna Abdullahi Ganduje na jihar ya kafa.

Da farko dai mun ji cewa Gwamnan Kano, Abdullahi Ganduje ya umarci duka hakiman dake jihar Kano da su bi sabbin sarakunan da suke ƙarƙashin su ba na Kano ba.

Darektan yaɗa labaran gwamna Ganduje Abba Anwar ne ya fitar da wannan sanarwa a madadin gwamnan.

Sanarwan ta gargaɗi dukka hakimai da su tsaya a masarautun su domin yin hawan Sallah.

“Gwamnatin Kano ta ƙaryata raɗe-radin da ake ta yadawa wai ta umarci hakimai su garzayo masarautar Kano domin yin hawan Daushe.

“Gwamnatin Kano bata da masaniya game da wannan sanarwa kuma ba daga gareta ya fito ba. Sakon gwamnati shine kowani hakimi ya yi hawa tare da sarkin kasarsa.

KU KARANTA KUMA: Hawan Sallah: Hakimai 11 sun yi watsi da umarnin Ganduje, sun yi biyayya ga sarki Sanusi II

“Hakiman dake ƙarkashin Bichi, za su yi hawa tare da sarkin Bichi ne, Hakiman Ƙaraye, suma da nasu sarkin da dai duka sauran hakiman masarautun da aka ƙirƙiro.

“Kada wani hakimi ya kuskura ya bi wani sarkin da ba a ƙarƙashin shi ya ke ba. Na Kano su bi na Kano haka sauran.”

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel