Jiya ba yau ba: Mai Martaba Sanusi II tare da Sarauniya Sa’adatu Bayero a shekarun baya

Jiya ba yau ba: Mai Martaba Sanusi II tare da Sarauniya Sa’adatu Bayero a shekarun baya

Wani tsohon hoto da a ka dauka shekarun baya ya shigo hannun Legit Hausa inda a ka ga Sarkin Kano na yanzu, Muhammadu Sanusi II tare da Uwargidansa a wajen wani taro.

A wannan hoto an ga Hajiya Sa’adiya Ado Bayero da Sahibin na ta zaune cikin wani gungun fararen fatar mutane inda su ka karkata fuskar su yayin da a ke daukar su wannan hoto.

Za a ga Mai martaba wanda a lokacin ya na Sanusi Lamido Sanusi sanye da wata bular riga irin ta Turawa mai Maballai a bude da kuma wata ‘yar bakar rigar jamfa ta gayu a cikin ta.

A gefe kuma Sarauniya a yau, Sa’adiya Ado Bayero ta na zaune da wata riga mai haske inda ta ke murmushi. Wannan hoto ya nuna Uwargidar cikin fara'a sanye da wasu ‘yan-kunne.

Ga wadanda ba su sani ba, Sarki Sanusi ya auri Sahibar ta sa ne shekaru 30 da su ka wuce. Sadiya Bayero ta auri Sanusi a lokacin ta na Budurwa mai shekara 15 da haihuwa a Duniya.

KU KARANTA: Sarkin Kano Sunusi II ya yi hawan Sallah a cikin ruwan sama

Jiya ba yau ba: Sanusi II tare da Sa’adatu Ado Bayero a shekarun baya
Sanusi Lamido Sanusi zaune da Sahibarsa a lokacin a na more soyayya
Asali: Facebook

Wani abin sha’awa shi ne Hajiya Sa’adiya Ado Bayero, Diya ce wurin Marigayi tsohon Sarki Ado Bayero, yayin da yanzu kuma Maigidan ta yake kan gadon mulkin Sarautar kasar Dabo.

Ba a san takamaiman lokaci da inda a ka dauki wannan hoto ba amma da alamu an yi hoton ne tun lokacin Sarkin ya na soyayya a wajen shekarun 1988 zuwa 1989 a Legas ko kasar waje.

Tun asali Sa’adiya Ado Bayero ‘Yar uwa ce wurin Sanusi Lamido Sanusi. Sarki Abdullahi Bayero shi ne wanda ya hafi Iyayensu, a ka kuma aura masu juna a lokacin su na Matasansu.

Sauran matan Sarkin su ne Hajiya Maryam Sanusi da kuma Rakiya Sanusi da kuma Sa'adatu Musatapha-Barkindo. Daga cikin ‘Ya ‘yan Sarki akwai Shahida, Ashraf da Siddika, dsr.

Jiya ba yau ba: Mai Martaba Sanusi II tare da Sarauniya Sa’adatu Bayero a shekarun baya
Uwargidar Sarkin Kano Hajiya Sa’adatu Ado Bayero a yau
Asali: Instagram

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel