Kasar Birtaniya Ta Aiko Sako Najeriya bayan APC Ta Sha Kaye a Zaben Gwamnan Jihar Osun
- Babbar Ofishin Jakadancin Birtaniya ya yaba da yadda aka gudanar da zaɓen gwamnan Osun tare da taya Ademola Adeleke murnar nasara
- Gwamnatin kasar Birtaniya ta ce ta lura da wasu alamomin ingantaccen tsarin dimokuraɗiyya yayin zaɓen da aka kammala
- Ta kuma yi kira da a duba matsalolin da suka taso domin ƙara inganta gaskiya, haɗin kai da sahihancin zaɓe a Najeriya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigeria - Gwamnatin Birtaniya ta hannun Ofishin Jakadancinta a Najeriya ta yaba da yadda aka gudanar da zaɓen gwamnan Jihar Osun ranar Asabar, 15 ga watan Agusta, 2026.
Birtaniya ta kuma aika da sakon taya Gwamna Ademola Adeleke murnar sake zaɓe a matsayin gwamnan jihar Osun karo na biyu.

Source: Twitter
The Cable ta ce a wata sanarwa da ofishin ya fitar ranar Litinin, ya ce ya gana da masu ruwa da tsaki daban-daban kafin ranar zaɓe, sannan ya tura tawagarsa ta masu sa ido da aka amince da su.
Martanin Birtaniya kan zaben Osun
Sanarwar ta ce:
“Bisa abubuwan da suka lura da su, kuma daidai da sakamakon ƙungiyoyin sa ido masu zaman kansu, muna maraba da wasu alamomi masu ƙarfafa gwiwa na ingantaccen tsarin dimokuraɗiyya.”
Ta ce daga cikin abubuwan da aka lura da su akwai buɗe rumfunan zaɓe a kan lokaci a wurare da dama, jajircewar jami’an tsaro wajen tabbatar da zaman lafiya da yadda jami’an Hukumar INEC suka aiwatar da tsarin zaɓe yadda ya kamata.
“Fiye da komai, mun samu ƙwarin gwiwa daga haƙuri, jajircewa da kuma yadda masu zaɓe suka shiga aikin zaɓe a tsawon ranar,” in ji sanarwar.
An lura da wasu matsaloli a zaben
Ofishin Jakadancin Birtaniya ya ce ya tura da rahotannin wasu matsaloli da suka faru a wurare daban-daban waɗanda suka haifar da tashin hankali kafin da kuma yayin gudanar da zaɓen.
Daga cikin matsalolin akwai katsalandan ga masu zaɓe, sayen ƙuri’u daga jam’iyyu daban-daban, ƙarancin damar zaɓe ga masu nakasa da tsofaffi, da kuma cunkoso sakamakon saurin aiki da ƙarancin na’urorin BVAS.
Ofishin ya buƙaci hukumomin da abin ya shafa su duba waɗannan matsaloli da kyau tare da ɗaukar darussan da za su ƙara amincewar jama’a, gaskiya da ɗaukar alhaki, kamar yadda Guardian ta rahoto.

Source: Facebook
Birtaniya ta yi magana kan zaben 2027
“Duk da haka, muna fatan darussan da aka samu daga zaɓen Osun za ta taimaka wajen samar da ƙarin gyare-gyare da za su ƙarfafa sahihanci, haɗin kai da amincewa da tsarin zaɓe na gaba,” in ji sanarwar.
Ofishin ya ce Birtaniya na ci gaba da jajircewa wajen aiki tare da hukumomin zaɓe na Najeriya, ƙungiyoyin farar hula da sauran abokan hulɗa domin tallafa wa zaɓuɓɓuka masu zaman lafiya, gaskiya, haɗin kai da sahihanci.
Dalilin faduwar APC a zaben Osun
A wani labarin, kun ji cewa jam'iyyar APC ta yi nazari kan zaben gwamnan jihar Osun kuma ta gano manyan dalilan da suka jawo mata rashin nasara.
APC ta amince cewa rikicin cikin gida, rashin jituwa kan dan takararta da kuma raina karfin masu kada kuri’a sun taimaka wajen kayar da ita a zaben gwamnan jihar Osun na 2026.
Asali: Legit.ng

