Gwamnan Osun Ya Yi Wuf Ya Karyata ADC da Ta Ce Sun Hada Kai a Doke APC
- Ademola Adeleke ya bayyana cewa nasararsa a zabe ta fito ne daga goyon bayan al’umma ba tare da sa hannun ADC ba
- Kakakin jam'iyyar ADC na kasa ya yi ikirarin cewa sun haɗa kai da jam'iyyar Accord don hana ‘dan takaran APC samun nasara
- Gwamnan ya nanata cewa yanzu shi shugaban kowa da kowa ne a jihar, ba tare da la'akari da bambancin jam'iyya ko addini ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada
Osun - Gwamna Ademola Adeleke na jihar Osun, ya karyata labarin da ya fara yawo a yanzu na cewa sun hada kai da ADC.
Mai girma gwamnan ya ce sam babu wata yarjejeniya da suka shiga da ‘yan jam’iyyar ADC da nufin doke APC a zaben jihar Osun.

Source: Twitter
Gwamnan ya yi wannan karin-haske ne a shafinsa na X a ranar Talata 18 ga watan Agusta 2026 da karfe 4:13 na yamma.
Mai girma Ademola Adeleke ya ce ADC ba ta cikin jam’iyyun siyasar da suka goyi bayan tazarcen shi a zaben ranar Asabar.
Gwamna Ademola Adeleke ya karyata ADC
Wannan ya karyata zancen da aka ji ya fito daga Kakakin ADC na kasa, Bolaji Abdullahi wanda ya ce an yi hadaka a takarar da aka yi.
Bolaji Abdullahi ya yi ikirarin sun hada-kai da jam’iyyar Accord domin tabbatar da cewa APC ba ta yi nasara a zaben gwamnan ba.
Kakakin gwamnan Osun, Olawale Rasheed ya fitar da sanarwa yana cewa mutanen Osun da abokan siyasarsa ne suka ba shi nasara.
Daily Trust ta ce jawabin Olawale Rasheed ya ruwaito gwamnan karara yana cewa babu rawar da jam’iyyar hadakar ta taka a galabar da ya yi.
"Ban shiga wata alaka ko yarjejeniyar zabe kafin, a lokaci ko bayan takarar gwamna ba.
Nasarar tana ga Ubangiji Madaukaki da mutanen kirki na jihar Osun na gagarumar goyon bayan tazarcenmu."

Kara karanta wannan
Abin da ADC ta yi da ya taimaka wajen kayar da jam'iyyar APC a zaben gwamnan Osun
Sannan gwamnan ya ce:
“Ina jinjina wa abokan siyasa wadanda suka fito gaba daya domin ganin Asabar ta zama ranar galaba wajen mutanen Osun.
Amma dole mu yi karin haske domin darajar tarihi cewa ADC ba ta taba kasancewa cikin kawancen mu.
Aikin da yake gaban Gwamnan Osun
Yanzu da aka gama zabe, Adeleke ya ce zai zama gwamna na kowa ba tare da la’akari da sabanin siyasa, addini ko kuma kabila ba.
A karshe kuma Adeleke ya ce aikin da yake gaban sa shi ne hada-kan al’umma tare da yin aiki tukuru wajen ganin cigaban jihar Osun.
Me ya faru da ADC a Osun?
Kun karanta rahoto cewa wani tsohon hadimin shugaba Muhammadu Buhari ya fito da hakikanin abin da ya faru a zaben gwamnan Osun.
Babafemi Ojudu ya yi rubutu kan abin da ya sa karfin jam’iyya bai yi tasiri a zaben Osun ba da rubdugun da aka yi wa sakataren ADC.
Sanata Ojudu ya ce an samu wadanda suka yaki Rauf Aregbesola da 'dan takaransa, suka taimaka wa takarar Accord maimakon jam'iyyarsu.
Asali: Legit.ng

