Tinubu Ya Gana da Shugaban EFCC da Minista game da Kadarorin da aka Kwace

Tinubu Ya Gana da Shugaban EFCC da Minista game da Kadarorin da aka Kwace

  • Shugaba Bola Tinubu ya gana da shugaban EFCC da ministan gidaje kan hanyar da sarrafa da sayar da gidajen da aka kwace
  • Ganawar ta zo ne kwanaki uku bayan Ademola Adeleke ya sake lashe zaben gwamnan Osun da kuma janye karar da jihar ta shigar kan EFCC
  • Shugaban kasa Tinubu ya taba umartar EFCC da ta janye umarnin da ta samu na daskarar da asusun gwamnatin Osun lamarin da ya jawo maganganu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Abuja – Shugaban Najeriya, Bola Tinubu, ya karbi bayanai daga shugaban Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta EFCC, Ola Olukoyede.

Haka kuma ya gana da Ministan Gidaje da Raya Birane, Muttaqha Rabe Darma, a fadar shugaban kasa da ke Abuja ranar Talata 18 ga watan Agusta, 2026.

Kara karanta wannan

Sojoji sun sauya taku, an tura zazzafan gargadi ga 'yan ta'adda

EFCC ta gana da shugaban EFCC
Shugaban kasa Bola Tinubu, Ola Olukayode Hoto: Bayo Onanuga/Economic and Financial Crimes Commission
Source: Twitter

Jaridar Punch ta wallafa cewa ganawar ta mayar da hankali kan yadda za a gudanar da harkokin gidajen da EFCC ta kwace a sassa daban-daban na Najeriya da kuma tsarin sayar da su bisa ka’idojin gaskiya da rikon amana.

Abin da Tinubu ya gana da EFCC

A ruwayar The Nation Olukoyede da Darma sun gana da Tinubu domin tattauna batun kula da gidajen da aka kwace da kuma yadda za a sayar da su.

Duk da ba a fitar da cikakken bayani game da abubuwan da aka tattauna ba, ana sa ran za a bayar da sauran batutuwa a nan gaba.

An gana kan yadda za a sarrafa gidajen da EFCC ta kwace
Shugaban Najeriya Asiwaju Bola Tinubu Hoto: Ajuri Ngelale
Source: Getty Images

Wannan anawa ita ce karon farko da Tinubu da Olukoyede suka fito fili tare tun bayan takaddamar da ta kunno kai kan matakin EFCC na daskarar da asusun gwamnatin Osun.

A ranar 5 ga Agusta, 2026, EFCC ta samu umarnin kotu na daskarar da asusun gwamnatin Osun. Hukumar ta ce matakin na da alaka da binciken zargin karkatar da kudaden gwamnati.

Kara karanta wannan

Yadda motoci suka nutse, komai ya tsaya cak bayan ambaliya a Abuja

Yadda aka kalubanci EFCC

Gwamnatin Osun ta kalubalanci matakin a gaban Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja, inda ta nemi soke umarnin tare da neman N2bn a matsayin diyya.

Bayan kwana biyu, Tinubu ya umarci EFCC da ta koma kotu ta janye umarnin daskarar da asusun. Shugaban kasar ya ce ya ji matukar kunya ba saboda EFCC ta yi amfani da hurumin da doka ta ba ta ba, amma saboda lokacin da aka dauki matakin, wanda ya zo kwanaki 10 kafin zaben gwamnan Osun.

Ganawar Tinubu da Olukoyede da Darma ta zo ne kwanaki uku bayan nasarar Adeleke da kuma janye karar gwamnatin Osun.

Tinubu ya gana da Akpabio

A wani labarin mun wallafa cewa Shugaban kasa, Bola Tinubu na ganawa da Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, a fadar shugaban kasa da ke Abuja a ana jajiberin fara yakin neman zabe.

Sanata Godswill Akpabio ya isa harabar ofishin shugaban kasa da misalin kusan 6:12 na yammacin Talata 18 ga watan Agusta, 2026 sannan ya isa wurin taron da Bola Ahmed Tinubu.

Ganawar na zuwa ne sa’o’i kadan kafin fara yakin neman zaben 2027 a hukumance ranar Laraba, 19 ga Agusta domin fara shirin kada kuri'a bayan hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa ta dage haramcin kamfen.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng