Bikin Sallah: Hoton Matan Sarkin Kano hudu tare da juna

Bikin Sallah: Hoton Matan Sarkin Kano hudu tare da juna

Yayin da babban Sarki Muhammadu Sanusi na II ya ke cabawa wajen hawan babbar sallah a birnin Kano, ba a bar Iyalinsa a baya ba inda mu ka samu wani hotonsu a Ranar idi.

An dauki hoton Matan Matan Mai martaba Sarkin Birnin Kano watau Malam Muhammadu Sanusi II ne a Ranar Lahadi, 11 ga Watan Agusta, 2019 a cikin fadar Sarkin Kano.

An fara buga wannan hoto na Matan Mai Martaban a shafin Linda Ikeji. Duka Matan Sarkin su na tare, daga ciki har da sabuwar Amaryar Sarki wanda ta tare kwanan nan.

Matan Sarki Sanusi II hudu ne a Duniya yanzu. Hajiya Sadiya Ado Bayero ita ce Uwargida. Sai kuma Sarauniyoyinsa Hajiya Maryam Sanusi da kuma Rakiya Sanusi.

KU KARANTA: Ganduje da Sarki Sanusi II sun hadu a wajen sallar idi

Bikin Sallah: Hoton Matan Sarkin Kano hudu tare da juna
Matan Sarkin Kano; Sa'adatu, Sadiya, Rakiya da Maryam
Asali: Twitter

Sarauniya Sa'adatu Musatapha-Barkindo ce matar Sarki ta hudu. Sa’adatu Barkindo, Diyar Lamidon Adamawa ta tare ne a Ranar Lahadi 4 ga Watan Agusta, 2019.

Mai martaba Sarkin Birnin Kano mai shekaru 58 ya auri Diyar Takwaransa na Adamawa ne tun shekaru biyar da su ka wuce amma sai yanzu ta tare bayan gama Jami’a.

Uwargidar Muhammadu Sanusi II ‘Diya ce wurin Marigayi Sarkin Kano watau Alhaji Ado Bayero. Sarkin ya auri ‘Yaruwar ta sa ne shekaru fiye da 20 da su ka wuce.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel