Miji, mata da jaririnsu sun mutu a cikin gidansu da wasu saka wa wuta a Kano

Miji, mata da jaririnsu sun mutu a cikin gidansu da wasu saka wa wuta a Kano

Wani iftila'i ya faru a garin Kano, ranar Laraba, yayin da wasu mutane suka kashe rai uku ta hanyar rufe su a cikin gida tare cinna wa gidan wuta.

Rahotanni sun ce sai da mutanen suka rufe Miji, Mata da Jaririyarsu a cikin gidan, sannan suka cinna wa gidan gaba dayansa wuta.

Wani shaidar gani da ido ya ce lamarin ya faru ne da duku-dukun safiyar ranar Laraba a unguwar Gayawa da ke yankin karamar hukumar Ungogo.

Duk kokarin makwabta na kokarin karya kofar gidan domin a shiga a ceto su bai yi tasiri ba saboda hucin wutar da ke fito wa daga gidan.

Shaidun gani da ido sun shaida wa manema labarai cewa gidan ya dade yana ci da wuta da tsakar daren, kamar yadda Jaridar The Nation ta wallafa.

DUBA WANNAN: A karshe: 'Yan Kwankwasiyya sun yi magana a kan zarginsu da cin mutuncin Pantami

Kakakin hukumar kashe gobara a jihar Kano, Sa'idu Ibrahim, ya ce wani mutum mai suna Mudassir Abdullahi ya kira su da misalin karfe 3:57 na dare domin sanar da su a kan tashin gobara a wani gida da ke unguwar Gayawa

"Bayan isar jami'an mu da misalin karfe 4:08 na safe, sun balle kofar gidan, sun tarar da mai gidan; Aminu Bala, matarsa; Rukayya Aminu, da jaririyarsu mai shekaru biyu; Aisha Aminu, sun samu munanan raunuka.

"Jami'an mu sun garzaya da su asibitin Murtala Muhammad, inda likita ya tabbatar da cewa sun mutu," a cewar Ibrahim.

Kazalika, kakakin rundunar 'yan sandan jihar Kano, DSP Haruna Kiyawa, ya tabbatar da faruwar lamarin tare da bayyana cewa kwamishinan 'yan sandan jihar, Ahmed Iliyasu, ya bayar da umarnin a fara binciken yadda wannan abun bakin ciki ya faru.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel