Za a Fara Yakin Neman Zabe, Tinubu Ya Aika Sako ga 'Yan Takara da Jam'iyyunsu

Za a Fara Yakin Neman Zabe, Tinubu Ya Aika Sako ga 'Yan Takara da Jam'iyyunsu

  • Tinubu ya bukaci jam’iyyu da ’yan takara su guji tashin hankali da kalaman rarrabuwar kawuna gabanin zaben 2027
  • Shugaban kasar ya bukaci ’yan siyasa su mayar da hankali kan manufofi da dabarun da za su amfani ’yan Najeriya
  • Tinubu ya ce ba a yi zabe don a mutu ko ai rai ba,, inda ya bukaci a fifita muradun Najeriya kan burin kashin kai

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Shugaba Bola Tinubu ya bukaci jam’iyyun siyasa da ’yan takararsu su guji tashin hankali da kalaman da ke raba kan jama’a gabanin babban zaben 2027.

Tinubu ya bayyana hakan ne ranar Talata a Abuja yayin rattaba hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya gabanin zaben 2027.

Tinubu ya aika sako ga 'yan takara
Shugaban kasar Najeriya, Bola Ahmed Tinubu Hoto: Bayo Onanuga
Source: Facebook

Hadimin shugaban kasa, Dada Olusegun, ya sanya jawabin shugaban kasar a shafinsa na X ranar Talata, 18 ga watan Agustan 2026.

Kara karanta wannan

Duk da shan wahala a zaɓen Osun, Davido ya faɗi yadda Tinubu zai yi nasara a 2027

Mai girma Bola Tinubu ya bukaci ’yan siyasa kada su yi amfani da kabilanci ko addini wajen yakin neman zabe, sai dai su mayar da hankali kan gabatar da ingantattun ra’ayoyi da manufofi ga ’yan Najeriya.

Me Tinubu ya gayawa 'yan takara?

Shugaban kasar, wanda George Akume, sakataren gwamnatin tarayya, ya wakilta a wajen taron, ya ce bai kamata a dauki zabe a matsayin abin da sai an yi nasara ko a mutu ba, inda ya bukaci masu ruwa da tsaki a siyasa su fifita muradun kasa kan burinsu na kashin kai da na jam’iyya.

"Abu ne da aka saba yayin yakin neman zabe mu samu sabani a matsayin abokan hamayya tare da gabatar da manufofi daban-daban na yadda za a tafiyar da kasarmu."
"Za mu iya yin wasu kalamai na siyasa a tsakaninmu. Amma a matsayinmu na ’yan gida daya, ’yan kasa daya, bai kamata mu taba komawa ga kalaman kabilanci ko addini na rarrabuwar kai a matsayin hanyar neman mulki ba.”

Kara karanta wannan

Peter Obi ya yi karatun ta natsu, ya ba 'yan siyasa shawara kan zaben 2027

“Mu tuna cewa zabe ba batun ko a yi nasara ko a mutu ba ne. Mu abokan hulda ne a aikin gina kasa. Ko mun ci ko mun sha kaye, Najeriya ce ya kamata ta zama babbar mai nasara.” In ji shi.

Tinubu zai bi yarjejeniyar da aka kulla

Shugaban kasar na Najeriya ya ce gwamnatinsa da jam’iyyar APC sun himmatu wajen bin yarjejeniyar zaman lafiya.

“Yayin da lokacin yakin neman zabe ke farawa, na sadaukar da kaina da jam’iyyata, All Progressives Congress (APC), wajen bin ka’idojin wannan yarjejeniya,” in ji shi.
“Mu yi yakin neman zabe ne bisa ingantattun ra’ayoyi. Mu yi muhawara kan batutuwa sannan mu inganta manufofin da suka fi dacewa wajen fadada damarmaki ga al’ummarmu da kuma hanzarta tafiyar Najeriya daga kasa mai tasowa zuwa kasa ta farko a duniya.” In ji shi.

Shugaban kasar ya bukaci sauran jam’iyyun siyasa da masu ruwa da tsaki a harkar siyasa su dauki irin wannan alkawari gabanin babban zaben 2027.

Tinubu ya yi muhimmin kira ga 'yan takara
Shugaba Bola Ahmed Tinubu zaune a ofis Hoto: @aonanuga1956
Source: Facebook

Davido ya hango nasarar Tinubu

A wani labarin kuma, kun ji cewa fitaccen mawaki, Davido ya ce zai iya yin caca da kuɗinsa kan sake zaɓen Shugaba Bola Ahmed Tinubu a 2027.

A cewarsa, ‘yan siyasa da dama daga Kudu sun riga sun nuna sha’awar tsayawa takarar shugaban ƙasa, lamarin da ke sa ‘yan adawa kasa gabatar da haɗin kai wajen ƙalubalantar Tinubu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng