Tsige Maja Sirdin Sarki ta janyo cece kuce da nuna ma juna yatsa a fadar Sarkin Kano

Tsige Maja Sirdin Sarki ta janyo cece kuce da nuna ma juna yatsa a fadar Sarkin Kano

Tun bayan bayyana rahoton dake nuna cewa mai martaba Sarkin Kano, Muhammadu Sunusi II ya tsige guda daga cikin bafadensa, watau Maja Sirdi, Alhaji Auwalu Idi, batun ya tayar da kura a fadar masarautar Kano.

Rahotanni sun bayyana cewa Sarki ya tsige Maja Sirdi ne sakamakon bayyana farin cikinsa da yayi da samun nasarar gwamnan jahar Kano, Abdullahi Umar Ganduje a kotun sauraron kararrakin zabe.

KU KARANTA: Shaidanun gwamnoni ne kadai za su saci dukiyar talakawansu - Abdullahi Sule

Haka zalika rahotannin sun kara da cewa Sarkin ya umarci maja sirdi daya tattara komatsansa daga fadar ya fice tare da iyalansa gabaki daya, gidan daya shafe sama da shekaru 30 a ciki, sa’annan ya mika makullan garken dawakan sarkin.

Jaridar KanoFocus ta ruwaito maja sirdin ya tabbatar da tsigeshi a kan wannan laifi da Sarkin ke tuhumarsa da aikatawa, inda yace shamakin Kano, Wada Jalo ne ya umarci ya tashi daga gidan a da yawun Sarki.

“Na halarci taron gangamin murnar samun nasarar gwamnan ne, inda ma na rabar da ruwan gora ga magoya bayan gwamnan, har ma na sanya ma gwamnan alkyabba, ashe yan fada basu ji dadin abinda na yi ba, don haka suka kudurci hukunta ni.

”Bayan kammala taron, sai Shamaki ya kirani, inda ya umarcina shiga na kirga masa adadin dawakan Sarki da kuma sauran kayayyakin dawakan, bayan na dawo masa da bayani, sai yace na bashi makullan gidan, kuma na fita daga gidana dake cikin gidan sarautar ba tare da bata lokaci ba, a yanzu haka ina neman gida ne kafin na tashi.” Inji shi.

Sai dai shugaban ma’aikatan gidan sarautar, Munir Sunusi ya musanta batun maja sirdi, inda yace: “Bani da wata masaniya game da ikirarin maja sirdi, amma dai na san mun kwace makullan ne bayan sace wasu sirdunan dawakan Sarki, Sarki bashi da wata matsala da maja sirdi, Shamaki ne ke kula dasu.

“Shamaki ya dauki wannan mataki ne bayan samun korafe korafen yawan bacewar sirdunan Sarki, don haka aka kwace makullan har sai bayan kammala bincike, babu wata maganan an tsigeshi saboda ya taya gwamna murna, kuma babu wanda ya tasheshi daga gidan da yake ciki, har yanzu shine maja sirdi.”

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel