Taurin Kan da Davido Ya Yi wa Dangote da Akpabio Lokacin Zaben Gwamnan Osun

Taurin Kan da Davido Ya Yi wa Dangote da Akpabio Lokacin Zaben Gwamnan Osun

  • A karshen makon jiya David Adeleke ya yi amfani da X yana zargin ana so a murde zaben gwamna a Osun
  • Manyan mutane har da Aliko Dangote da Shugaban majalisar dattawa sun bukaci ya goge abin da ya wallafa
  • Mawakin ya yi kunnen-kashi, ya ce ba zai goge rubutun nasa ba har sai INEC ta fadi sakamakon zaben gwamnan

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada

Osun - Shahararren mawaki, David Adeleke wanda ake kira Davido ya yi magana kan rawar da ya taka a zaben jihar Osun.

Lokacin ana zaben gwamnan Osun, mawakin ya yi ta sakin bayanai a shafinsa na X wanda jama’a suka fi sani da Twitter a baya.

Davido
Aliko Dangote, David Adeleke 'Davido' da Godswill Akpabio Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Dangote, Akpabio sun kira Davido a waya

A wata hira da aka yi da shi da yanzu yake shafin News Central TV a X, Davido ya fadi yadda ya jawo magana da rubutunsa.

Kara karanta wannan

Bayan kin bayar da hakuri, Davido ya yi barazana ga gwamnan APC

Lokacin da ya saki wasu bayanai a shafin sada zumunta na zamani, sai da ta kai manya irinsu Aliko Dangote sun kira shi ta tarho.

Baya ga attajirin Afrikan, Shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio ya tuntube shi a waya domin ya goge rubutun da ya yi.

Davido ya zargi Akpabio da kiran masu tattara sakamakon zaben gwamnan Osun, yana nuna alamun cewa ana so a tafka magudi.

Duk da kiran shi da aka yi, mawakin ya ki goge wadannan bayanai, ya ce ba zai yi ba har sai INEC ta tabbatar da nasarar kawunsa.

"Na ji Shugaban majalisa yana neman ya kira wurin tattara sakamakon zabe. Su na kira na in goge rubutun Twitter, na ce ku yi hakuri fa. Mutanen nan kun ja layi da kawu na…ba zan iya goge komai ba.
"Kawu Dangote ma ya kira. Na ce kawu ba zan goge ba sai INEC ta fitar da sanarwa...

Kara karanta wannan

Tinubu da wadanda suka agaji jam'iyyar Accord ta yi galaba a zaben jihar Osun

- Davido

Davido ya zargi APC da kashe N100bn

Baya ga abin da ya faru lokacin da ake tsakiyar tattara sakamako, mawakin ya zargi ‘yan jam’iyya mai mulki da wasa da kudi a zaben.

A cewarsa ‘yan adawar gwamna Ademola Adeleke sun batar da kimanin N110bn domin canza sakamakon zaben ranar 15 ga Agusta.

Mawakin ya ce:

"Yau na tabbatar da cewa sun kashe N110bn. Na samu labari daga wata majiya…idan ku ka ga kudin da mutanen nan suka zo da shi, da a ce sun samu yadda suke so a zaben nan, da Najeriya ta mutu.
"Domin kuwa da kudi da tada rikici zai zama dabarar lashe zabe."

A bangarensu, Davido ya ce ba su kashe kudi a sayen kuri’u ba, illa suka dogara da addu’ar mutane su ci kudin kuma su zabi jam'iyyar Accord.

Morris Monye ya wallafa bangaren hirar:

Adeleke: ‘ADC, ba haka ba ne’

Gwamna Ademola Adeleke ya karyata cewa sun yi yarjejeniya da ADC a zaben jihar Osun kamar yadda labari ya gabata a ranar Talata.

Kara karanta wannan

Hadimin Buhari ya fito da hakikanin abin da ya faru a zaben gwamnan Osun

Gwamna Ademola Adeleke ya ce bai shiga wani ƙawance da jam’iyyar ADC a zaɓen gwamnan jihar Osun ba, akasin abin da ake yadawa.

Bolaji Abdullahi wanda yake magana da yawun ADC ya ce jam'iyyarsu ta zo ta uku ne saboda sun goya wa takarar Accord baya ranar Asabar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng