Bikin Sallah
Tsohon Shugaban kasa Goodluck Jonathan ya yi wa al’ummar Musulmai addu’ar barka da sallah. Shugaba Goodluck Jonathan ya yi sammakon aika wannan sako ne a jiya.
Gwamnatin Kaduna a karkashin Gwamna Nasir Ahmad El-Rufai ta sanya dokar hana fita da zirga zirga ne a jahar domin dakile yaduwar annobar Coronavirus mai kisa.
Mun kawo maku bidiyo na fitowar Mai Martaba Sarki Muhammad Sanusi yayin Gabatar Da Sallar Eid a Gidan sa da ke Garin Lagos a yau 1 ga Shawwal 1441 AH/2020.
A jiya ne Shugaba Buhari ya nemi ‘Yan Najeriya su kara hakuri da dokokin da aka sa saboda COVID-19. Buhari ya ce takunkumin ya takaita ibada da haduwar jama’a.
Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana cewa a karamar sallar bana, shi da iyalinsa za su gudanar da sallar Idinsu ne a gida kamar yadda Garba shehu ya bayyana.
Duk da cigaba da ruruwan annobar Coronavirus tare da hauhawar adadin mutanen dake kamuwa da cutar a duk rana, wasu jahohi sun sassauta doka don jama’a su huta.
Gwamnatin jahar Kaduna ta tabbatar da dokar hana fita da shiga jahar Kaduna, sa’annan ta dauki alwashin tabbatar da dokar hatta a ranar karamar Sallah na bana.
Yanzu nan mu ke jin cewa Gwamnatin Tarayya ta bayyana ranakun hutun karamar Sallar bana. Mista Ogbeni Rauf Aregbesola, ya yi jawabi a madadin shugaban kasa.
Kungiyar Jama’til Nasril Islam JNI, a karkashin jagorancin mai alfarma Sarkin Musulmi ta yi bayani game da sabon salon sallar Idi da za’a yi a karamar sallah.
Bikin Sallah
Samu kari