Masana'antar Fim Ta Yi, Jarumin da Ya Shahara Ya Bar Duniya
- Jarumin fina-finan Najeriya, Francis Duru, ya rasu yana da shekara 57 bayan fama da gajeriyar rashin lafiya
- Duru ya shahara sosai bayan fitowa a fim ɗin Rattlesnake na shekarar 1995, inda ya taka rawar Ahanna
- Fitaccen jarumin ya bar matarsa Adokiye da ’ya’ya huɗu, bayan sun yi aure a shekarar 2003, inda daya daga cikinsu ya mutu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Legas - Fitaccen jarumin fina-finan Najeriya, Francis Duru, ya rasu yana da shekara 57 a duniya.
yalansa ne suka sanar da rasuwarsa, inda suka bayyana cewa ya rasu ne bayan fama da gajeriyar rashin lafiya.

Source: Instagram
An tabbatar da rasuwar Francis Duru
Iyalan na fitaccen jarumin fina-finan sun sanar da rasuwarsa ne a shafinsa na Instagram da sanyin safiyar Juma’a, 23 ga watan Oktoban 2026.
A cikin sanarwar, iyalan sun ce:
“Mu, iyalan Francis Duru, muna sanar da rasuwarsa cikin alhini bayan fama da gajeriyar rashin lafiya.”
Sun kuma gode wa jama’a bisa addu’o’i, ƙauna da fahimtar da suka nuna musu, tare da addu’ar Allah Ya ba shi hutu na har abada.
Yadda Francis Duru ya fara harkar fim
An haifi Francis Duru a ranar 27 ga Yuli, 1969, a ƙasar Kamaru, ga iyayensa ’yan asalin Jihar Imo ta Najeriya, cewar rahoton jaridar TheCable.
Ya yi karatun firamare da sakandare a Kamaru, kafin ya dawo Najeriya domin neman ilimin jami’a.
Daga bisani, ya samu gurbin karatu a Jami’ar Fatakwal da ke Jihar Ribas, inda ya karanci fasahar wasan kwaikwayo, sannan ya kammala digirin farko a shekarar 1996.
Duru ya fara fitowa a masana'antar fina-finan Najeriya a shekarar 1989, a cikin fim ɗin Missing Mark, wanda marigayi Ndubuisi Oko ya bada umarnin shirya shi.
Sai dai fitowar tasa a fim ɗin ba ta sa ya samu shahara sosai a lokacin ba, domin ana kallonsa a matsayin sabon jarumi a masana'antar.
Fim ɗin Rattlesnake ya ƙara masa farin jini
Duru ya samu gagarumar karɓuwa a masana'antar a shekarar 1995, bayan fitowa a fim ɗin Rattlesnake, wanda marigayiya Amaka Igwe ta shirya.
A cikin fim ɗin, ya taka rawar Ahanna, wadda ta taimaka wajen ƙara masa suna a masana'antar fina-finan Najeriya.
A tsawon rayuwarsa ta sana'a, Duru ya samu lambobin yabo da karramawa da dama saboda gudunmawar da ya bayar a harkar nishaɗi.
An kuma naɗa shi jakadan zaman lafiya na Majalisar Ɗinkin Duniya saboda tasirinsa mai kyau ga matasa.
A shekarar 2020, ya lashe kyautar gwarzon jarumi a babban matsayi a ɓangaren fina-finan Igbo a bikin bayar da kyaututtukan Best of Nollywood Awards, saboda rawar da ya taka a fim ɗin Mboputa.
Ya bar mata da ’ya’ya 4
Marigayi Francis Duru ya auri matarsa Adokiye a shekarar 2003, kuma sun haifi ’ya’ya huɗu tare.
Sai dai iyalan sun taɓa fuskantar babban rashi a watan Agustan 2024, lokacin da suka rasa ɗaya daga cikin ’ya’yansu mai suna Ifeanyi.

Source: Instagram
Jagoran Afenifere ya rasu
A wani labarin kuma, kun ji cewa dattijon ƙasa kuma jagoran ƙungiyar Afenifere, Pa Reuben Famuyide Fasoranti, ya rasu yana da shekaru 100 a duniya.
Gwamna Aiyedatiwa na Ondo ya miƙa ta’aziyyarsa ga iyalan Fasoranti, al’ummar masarautar Akure da kuma daukacin jihar.
Asali: Legit.ng


