"Kai ne Masar," Atiku Ya Maida Martani bayan Tinubu Ya Yi Misali da Tarihin Annabi Musa AS
- Atiku Abubakar ya ce kwatanta cire tallafin fetur da wani bangaren tarihin Annabi Musa ya nuna yadda Tinubu bai fahimci wahalhalun da ’yan Najeriya ke ciki ba
- Tsohon mataimakin shugaban ƙasar ya ce zai rage tsadar rayuwa ta hanyar tallafa wa kayayyakin man fetur da aka tace a Najeriya kawai
- Atiku ya soki gwamnatin Tinubu kan matsalar rashin tsaro, yana mai cewa dole ne shugaban ƙasa ya kare rayuka da dukiyoyin al’umma
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigeria - Ɗan takarar shugaban ƙasa na ADC, Atiku Abubakar, ya ce kwatanta cire tallafin fetur da tseratar da Annabi Musa da Shugaba Bola Tinubu ya yi ya nuna “yadda bai fahimci wahalhalun da ’yan Najeriya ke ciki ba.”
Atiku ya ce Tinubu ya yi alfahari da cire tallafin fetur a ranar farko da ya hau mulki, “kamar azzalumin sarki da ke tuna wahalhalun da ya jefa mutane a ciki yana mai ɗaukar hakan a matsayin nasara.”

Source: Facebook
Daily Trust ta rahoto cewa ya fadi haka ne a cikin wata sanarwa da Phrank Shaibu, Daraktan Yaɗa Labarai da Sadarwa na Yaƙin Neman Zaɓen Shugaban Ƙasa na ADC, ya fitar a madadinsa.
Atiku ya maida martani ga Tinubu
Atiku ya ce:
"Bola, kai ne Masar ɗin da ’yan Najeriya ke ƙoƙarin tserewa. Kana murna da ranar da ka ƙara tsadar mai, sannan ka yi wa iyalan da ke fama da wahalar biyan kuɗin abinci da sufuri wa’azi kan dalilin da ya sa bai kamata su koma baya ba.
“Aƙalla Fir’auna ya san yana tsare mutane a zaman fursunoni. Tinubu yana kallon iyalai suna rage yawan abincin da suke ci, ma’aikata suna kashe albashinsu a sufuri, sannan ’yan kasuwa suna fama da biyan kuɗin lantarki, amma sai ya ba su labarin Annabi Musa.
“Wataƙila yana ambaton nassosin addini, amma yana mulki kamar Fir’auna, Hirudus da Ahab a haɗe: bai damu da kukan jama’a ba, yana alfahari da wahalhalun da ya jefa su a ciki, kuma yana ganin cewa kasancewarsa a kan mulki ya ba shi damar kauce wa amsa tambayoyi kan abin da ya aikata.

Kara karanta wannan
Yari: Idan Buhari ya gaza magance matsalar tsaron Najeriya, me ku ke tunani daga Tinubu?

Source: Twitter
Atiku ya yi alkawarin kawo sauki
Atiku ya kuma bayyana cewa a halin da ake ciki yan Najeriya ba tarihi suke bukata daga wurin shugaban kasa ba face samar masu da hanyar da za ta saukaka masu rayuwa.
“Bola, uwa da ke ƙoƙarin ciyar da ’ya’yanta ba za ta iya amfani da kwatanci wajen sayen abinci ba. Ma’aikaci ba zai iya zuwa wurin aiki da labarin Bahar Maliya ba. ’Yan Najeriya suna tambayar yadda za ka sa rayuwa ta zama mai sauƙi. Ka fito ka ba su amsa.
“Na shirya sake samar da sauƙin rayuwa ta hanyar tallafin da ’yan Najeriya za su ji amfaninsa a zahiri. Shawarata a bayyane take: a ware kayyadadden tallafi wajen samar da mai da tace shi a Najeriya kuma a sayar wa ’yan Najeriya kawai.
- Atiku Abubakar.
Atiku ya soki wasu nade-naden INEC
Kun ji cewa Atiku Abubakar, ya bayyana damuwarsa kan naɗa mutane biyu Yarabawa don jagorantar muhimman wurare a hukumar INEC.
Atiku ta bakin kakakin sa, Phrank Shaibu, ya buƙaci bayanin naɗin Oluyemi Titilayo Adeyemi-Showunmi da Dr. Lawrence Bayode a sashen ayyukan zaɓe da sashen ICT.
Asali: Legit.ng
