Bayan Zargin Son Pantami, Wike Ya Magantu kan Taimakon Wani Dan Takara
- Ministan Abuja, Nyesom Wike, ya musanta cewa ya goyi bayan Ishaku Abbo, ɗan takarar gwamnan Adamawa a jam’iyyar LP
- Wike ya bayyana cewa ba shi da wata alaka ta siyasa da jam’iyyar LP ko ɗan takararta a zaɓen gwamnan Adamawa
- Ministan ya buƙaci al’ummar Adamawa su yi watsi da rahoton ƙarya, yana mai cewa zai sanar da wanda yake goyon baya da kansa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
ABUJA - Nyesom Wike, ministan babban birnin tarayya Abuja (FCT), ya yi magana kan rade-radin goyon bayan wani dan takarar gwamna a Adamawa.
Wike ya musanta rahotannin da ke cewa ya amince da takarar Ishaku Abbo, ɗan takarar gwamnan Adamawa na jam’iyyar Labour (LP).

Source: Facebook
Hakan na cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Juma’a ta hannun Lere Olayinka, babban mataimakinsa kan harkokin yaɗa labarai na jama’a ya fitar a shafin Facebook.
Wike ya magantu kan alaka da Pantami
Wannan na zuwa ne bayan zargin da aka ce ana yi wa Wike wai yana taimakawa takarar Isa Ali Pantami a Gombe.
Nyesom Wike ya yi ikirarin cewa bai taba haduwa da tsohon ministan sadarwa kuma dan takarar PDP a jihar Gombe, Farfesa Isa Ali Pantami ba.
Ministan Abuja ya bayyana cewa gwamnan Gombe, Inuwa Yahaya na zarginsa da goyon bayan takarar gwamna da Pantami ke yi a PDP.
Wannan na zuwa ne yayin da Wike ke .usayar yawu da wasu daga cikin gwamnonin APC, wadanda ba su goyon bayan gamayyar da ya kirkiro.
Wike ya musanta alaka da Abbo
Ministan ya ce ba shi da wata alaka ta siyasa da LP ko wani ɗan takararta a Adamawa kamar yadda wasu ke yaɗawa.
Ministan ya bayyana cewa rahoton da aka yaɗa a kafafen sada zumunta, wanda ya jingina masa cewa ya buƙaci al’ummar Adamawa su yi zaɓi cikin hikima tare da cewa Abbo ne ya fi dacewa ya jagoranci jihar, ƙarya ne.
Wike ya buƙaci al’ummar Adamawa da su yi watsi da rahoton da aka yaɗa a kafafen sada zumunta, yana mai cewa shi da kansa zai sanar da ɗan takarar da yake goyon baya idan ya yanke shawarar bayyana matsayinsa.
Abbo ya koma jam’iyyar LP a watan Mayu bayan ya fice daga jam’iyyar African Democratic Congress (ADC) sakamakon rikicin shugabanci da ya addabi jam’iyyar a lokacin.
APC ta magantu kan rigima da Wike
A wani labarin, mun ba ku labarin cewa jam’iyyar APC ta musanta rahotannin rikici tsakanin gwamnoninta da Nyesom Wike, tana mai cewa babu wata takaddama tsakaninsu kan zaɓen 2027.
Felix Morka ya ce gwamnonin APC da Wike sun haɗu wajen tallafa wa Shugaba Bola Tinubu domin sake zaɓensa a babban zaɓen 2027.
Kakakin APC ya bayyana shigar ‘yan siyasa daga jam’iyyu daban-daban cikin kwamitin yaƙin neman zaɓen Tinubu a matsayin sabon mataki a dimokuraɗiyyar Najeriya.
Asali: Legit.ng

