COVID-19 ta taba mana rayuwa, addini, da sha'anin tattalin arziki – Inji Buhari

COVID-19 ta taba mana rayuwa, addini, da sha'anin tattalin arziki – Inji Buhari

A ranar Asabar, 23 ga watan Mayu, 2020, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce annobar COVID-19 ta yi wa ‘yan Najeriya illa a game da zamantakewa, tattalin arziki da addininsu.

A sakon barka da sallah da shugaban kasar ya aikawa musulman Najeriya, ya koka da yadda wannan cuta ta taba rayuwar Bayin Allah, ya ce da yanzu mutane sun barke da bikin sallah.

A daidai lokacin da azumin watan Ramadan ya kare, shugaba Buhari ya ce: “A karon farko a shekarun nan, annobar COVID-19 ta taba addini, zamantewa da kuma tattalin arzikinmu."

Duk da haka mai girma shugaba Muhammadu Buhari ya yi kira ga musulmai su jajirce, su zama masu imani. A yau Lahadi ne mafi yawan musulmai su ke bikin karamar sallah a Najeriya.

Da ya ke bada misalin yadda annobar Coronavirus ta yi tasiri wajen addinin al’umma, sai ya ce: “Azumin bana ya zo wa musulmai da kalubale saboda sun hakura da ibadan addinsu.”

KU KARANTA: Za mu baza Jami’ai saboda bikin sallah a Kaduna - ‘Yan Sanda

COVID-19 ta taba mana rayuwa, addini, da kuma tattalin arziki – Inji Buhari
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari. Hoto: Vanguard
Asali: UGC

Shugaban ya kara da cewa: “Ibadu wadanda su ka hada da sallar jami’i da aka saba da darasin tafsirin Al-Qur’ani mai girma, tare da tafiyar ziyarar kasa mai tsarki da ake yi na Umrah.”

Buhari ya ce dole ta sa aka yi hakan domin hana yaduwar COVID-19. Wannan jawabi ya fito ne ta bakin Malam Garba Shehu wanda ya ke magana a madadin shugaba Muhammadu Buhari.

A jawabin na Garba Shehu, ya yabi mutanen kasar da su ka bi dokokin da gwamnati ta ka kawo na takaita yaduwar wannan cuta. Ya ce: “Na san halin da wannan mataki ya jefa jama’a.”

“Bari in yi amfani da wannan dama in yabawa kokarin da Musulmai da Kiristoci su ka yi na ba hukuma hadin-kai wajen dabbaka takunkumin zaman gida da kauracewa shiga cinkoso.”

“Babu gwamnatin da za ta kakaba wadannan dokoki masu wahala da gan-gan a kan jama’a, idan har ta na da wani zabi.” Buhari ya ce takunkumin ya takaita ibada da ma haduwar jama’a.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel