Yadda Jihohi, Kananan Hukumomi Ke Lamushe Kudin Yan Kasa Fiye da Tarayya

Yadda Jihohi, Kananan Hukumomi Ke Lamushe Kudin Yan Kasa Fiye da Tarayya

  • Ministan kuɗi, Taiwo Oyedele, ya ce jihohi da ƙananan hukumomi suna samun kusan kashi 85 cikin 100 na albarkatun Najeriya
  • Oyedele ya bayyana hakan duk da nauyin tsaro, tsaro na cikin gida, harkokin ƙasashen waje da zaɓe
  • Ya ce gwamnati na shirin miƙa wasu ayyuka ga jihohi, tare da ba su kuɗaɗe domin inganta ilimin firamare da noma

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Ministan kuɗi kuma mai kula da tattalin arziki, Taiwo Oyedele, ya bayyana yadda ake raba albarkatun Najeriya.

Oyedele ya ce jihohi da ƙananan hukumomi suna samun kusan kashi 85 cikin 100 na albarkatun Najeriya, yayin da gwamnatin tarayya ke samun kashi 15 duk da nauyin ayyukanta.

Minista ya kare matakan gwamnatin Tinubu
Ministan kudi, Taiwo Oyedele da Shugaba Bola Tinubu. Hoto: Bayo Onanuga.
Source: Facebook

Oyedele ya bayyana hakan ne ranar Laraba a wani taron tattaunawa da aka gudanar a Chatham House da ke Landan, cewar TheCable.

Kara karanta wannan

Duk da ƙoƙarin Tinubu kan tsadar kaya, abinci na ci gaba da tashi a kasuwanni

Nauyin ayyukan da ke kan gwamnatin tarayya

Ya ce gwamnatin tarayya ce matakin gwamnati mafi ƙarancin albarkatu idan aka kwatanta da nauyin ayyukan da take gudanarwa, ciki har da tsaro, tsaron cikin gida, harkokin ƙasashen waje da gudanar da zaɓe.

Ministan ya ƙara da cewa gwamnatin tarayya tana kuma shiga harkokin ilimin firamare da kula da lafiyar al’umma, don haka tana buƙatar ƙarin kuɗaɗe domin gudanar da ayyukanta yadda ya kamata.

Oyedele ya ce:

“Bisa ga bayanai, gwamnatin tarayya ce mafi ƙarancin albarkatu, duk da cewa ita ce take da mafi yawan nauyin ayyuka. Daga cikin albarkatun Najeriya, kusan kashi 85 cikin 100 ana warewa jihohi da ƙananan hukumomi, yayin da kashi 15 kawai ake bai wa tarayya.”

Ya kuma bayyana cewa gwamnatin tarayya ba ta karɓar harajin kuɗin shiga daga daidaikun mutane a Najeriya.

Kason da gwamnatin tarayya ke samu daga albarkatun kasa
Shugaba Bola Tinubu na Najeriya. Hoto: Asiwaju Bola Tinubu.
Source: UGC

Da yake magana kan rabon harajin kayayyaki da ayyuka (VAT), ya ce jihohi suna samun kashi 90 cikin 100 na kuɗaɗen, yayin da gwamnatin tarayya ke karɓar kashi 10.

Kara karanta wannan

Hakeem Baba Ahmed: Muhimman bangarori 2 da Shugaba Tinubu ya kunyata 'yan Najeriya

Ministan ya bayyana cewa jihohi suna riƙe da kuɗaɗen harajin tambari, yayin da gwamnatin tarayya ta dogara ne kawai da rabonta daga asusun tarayya.

Tsarin rabon kuɗaɗen shiga na Najeriya na yanzu yana ware kashi 52.68 ga gwamnatin tarayya, kashi 26.72 ga jihohi, sannan kashi 20.60 ga ƙananan hukumomi, cewar Punch.

Gwamnatin Tarayya na shirin ba jihohi wasu ayyuka

Oyedele ya ce gwamnatin tarayya na shirin miƙa wasu nauyin ayyuka ga jihohi, yana mai cewa jihohin sun fi dacewa su gudanar da wasu daga cikinsu, yayin da tarayya za ta inganta hanyoyin samun kuɗaɗen shiga ba tare da ƙara wa ’yan Najeriya nauyin kuɗi ba.

A ƙarƙashin shirin, ya ce gwamnatin tarayya za ta iya ba jihohi kuɗaɗe domin inganta ilimin firamare, tallafa wa harkokin noma da gina hanyoyin da za su haɗa gonaki da kasuwanni.

Minista ya fadi illar dawo da tallafi

Mun ba ku labarin cewa Ministan Kuɗi, Taiwo Oyedele, ya yi gargaɗin cewa dawo da tallafin fetur na iya jawo litar mai ta kai Naira 2,000.

Oyedele ya ce cire tallafin fetur ya samar da Naira tiriliyan 15.8 ga asusun tarayya tsakanin Yuni 2023 da Disamba 2025.

Gwamnatin tarayya na shirin rage haraji da kuɗaɗen hanya, tare da ƙara tallafin kuɗi ga marasa ƙarfi da rancen kasuwanci.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jarida ne da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.