Akwai Yiwuwar Ma’aikata Su Shiga Yajin Aiki, ba a Dace a Zaman da Aka Yi da Gwamnati ba
- Tattaunawar gwamnati da kungiyoyin kwadago ta kare ba tare da cimma matsaya kan bukatun ma’aikata ba
- NLC da TUC sun bukaci a rage farashin man fetur, sake duba mafi ƙarancin albashi kuma a biya bashin hakkoki
- Kungiyoyin sun fara zancen yiwuwar yajin aiki na kasa baki daya idan taro na gaba bai kawo abin da ake nema ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada
Abuja - Babu mamaki a yi fama da yajin aikin da zai karade ko ina duk da kokarin gwamnati na shawo kan ma’aikata.
Ba a cin ma wata nasara a zaman da aka yi tsakanin Gwamnatin tarayya da kungiyoyin kwadago na NLC da TUC a jiya ba.

Source: Getty Images
Zaman ma'aikata da Gwamnatin taraya
Leadership ta kawo rahoto cewa haka nan aka tashi babu matsaya a zaman da aka yi da shugabannin ma’aikata da ‘yan kasuwa.

Kara karanta wannan
Hakeem Baba Ahmed: Muhimman bangarori 2 da Shugaba Tinubu ya kunyata 'yan Najeriya
Wannan ya sa aka kara wa’adin kwana biyar a lokacin tattaunawar da gwamnati za ta yi da ma’aikatan domin biya masu bukata.
Har aka tashi zaman ranar Alhamis a Abuja, babu wasu kwararan matsaya da gwamnati ta iya cin ma tsakaninta da ‘yan kwadago.
Ma'aikata sun fara batun yajin-aiki
A dalilin haka kungiyoyin kwadagon suka fara aika wa da gargadi cewa muddin babu wata mafita, za su tafi yajin-aiki ne a kasar.
Lokacin da aka kara yana nufin ranar Talata 27 ga watan Oktoba za a sake zama tsakanin jami’an gwamnati da wakilan ma’aikata.
Abin da ya jawo zama da gwamnati
Tun 9 ga Oktoban 2026, NLC ta ba gwamnati wa’adin kwanaki 14 tana cewa idan ba a rage kudin man fetur ba, za a ga ba daidai ba.
Kungiyar ta kuma bukaci a koma tebur domin ganin an kara albashi tare da kawo wa jama’a saukin haraji kuma a biya bashin hakkoki.
An yi hakan da nufin sama wa ma’aikata sauki yayin da ake kukan tsadar rayuwa. Labarin ya zo a wani rahoto da Vanguard ta fitar.
NLC ta TUC sun fitar da sanarwar bayan taro
Duk da haka taron ranar Alhamis bai haifar da ‘da mai ido ba a dalilin zuwan jami’an gwamnati babu isasshen shiri da tanadi.
Bayan zaman da aka yi a Ma’aikatar kwadago, Sakatarorin NLC da TUC, Benson Upah da kuma Nuhu Toro sun fitar da jawabi.
Jawabin NLC da TUC ya ce gwamnati ta nemi karin lokaci domin tattaro shugabannin hukumomin da za a yi zama na gaba da su.
Shugabannin kwadagon sun yi gargadi ba za su yarda a yi ta bata masu lokaci ba tare da kira a fara shirin duk mai iya yiwuwa.

Source: Getty Images
Gwamnati ta waiwayi masu rijiyoyin mai
An samu rahoto cewa Gwamnatin Najeriya za ta soke lasisin rijiyoyin mai da ba su aiki kafin karshen watan Oktoban 2026.
Najeriya ta ci aniyar samun ganguna 250, 000 daga rijiyoyin mai sama da 20 da aka raba wa mutane a shekarar 2023 da 2024.
NUPRC ta yi hakan ne domin inganta tattalin arziki da kara yawan man da ake hakowa duk rana.
Asali: Legit.ng
