Bikin Idi: Babu aiki Ranar Litinin 25, Talata 26 – Inji Ministan cikin gida

Bikin Idi: Babu aiki Ranar Litinin 25, Talata 26 – Inji Ministan cikin gida

A yau Alhamis, 21 ga watan Mayu, 2020, gwamnatin Najeriya ta fitar da sanarwa ta musamman a game da bikin karamar sallah, inda ta bayyana ranakun hutu a fadin kasar.

Gwamnati ta tsaida ranar Litinin 25 da Talata 26 ga watan Mayun 2020 a matsayin ranakun murnar sallah. Ministan harkokin cikin gida ne ya bada wannan sanarwar dazu.

Mista Ogbeni Rauf Aregbesola, da ya ke wannan jawabi a madadin shugaban kasa, ya taya musulmai murnar kammala azumin watan Ramadan da ke daf da zuwa karshe.

Mai girma Ogbeni Aregbesola ya yi kira ga Musulmai su yi koyi da halayen Manzon Allah, Annabi Muhammad (SAW) na kirki, hakuri da kaunar makwabta da kuma zaman lafiya.

Gwamnatin tarayya ta nuna takaici a game da rikicin kabilancin da ake faye yi a arewacin Najeriya, inda ya yi kira ga jama’a su rika yi wa juna kallon cewa an zama daya.

KU KARANTA: CFII ta ce bana babu sallar idi a Garin Abuja

Ogbeni Aregbesola ya sake jaddadawa ‘yan kasar cewa gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari ta na bakin kokarin kawo karshen annobar COVID-19 da hadin kan mutane.

A jawabin ministan, gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari ta yaba da nasarorin da jami’an tsaro su ke samu a arewa maso gabas a yaki da ‘yan ta’addan Boko Haram.

Bayan haka, an bukaci mutane su guji shiga cinkoso, su kuma maida hankali wajen tsabtace jikinsu da muhallinsu, game da bin duk dokokin da hukumomi su ka sanya.

Ministan ya jawo aya daga cikin Al-Qur’ani wanda ta ce: “Ya ku wadanda ku ka yi imani, ku yi wa Allah da’a, ku bi Manzo da masu mulki daga cikinku. Kuma idan kun samu sabani, ku koma ga Allah da ManzonSa, idan har kun yi imani da Allah da ranar karshe.”

Sanarwar ta fito ne daga darektan yada labarai da hulda da ‘yan jarida na ma’aikatar, Mohammed Manga.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel