Dubi jerin jahohi 14 a Arewacin Najeriya da suka amince a gudanar da sallar Idi

Dubi jerin jahohi 14 a Arewacin Najeriya da suka amince a gudanar da sallar Idi

Duk da cigaba da ruruwan annobar Coronavirus tare da hauhawar adadin mutanen dake kamuwa da cutar a duk rana, wasu jahohi sun sassauta doka domin jama’a su dan sarara.

Daga cikin matakan sassauta dokar akwai gwamnatocin da suka bada umarnin bude Masallatai don baiwa Musulmai daman gudanar da sallar Idi, sallar Juma’a da sallolin farilla 5.

Legit.ng ta ruwaito akwai wasu jahohin Arewacin Najeriya guda 14 da suka bada izinin sassauta doka domin jama’a su fita su gabatar da sallar Idi. Ga jerin jahohin kamar haka;

KU KARANTA: Duk wanda ya shiga yajin aiki a bakacin aikinsa – El-Rufai ga jami’an kiwon lafiya

- Kogi

- Bauchi

- Kano

- Jigawa

- Katsina

- Adamawa

- Borno

- Gombe

- Benuwe

- Neja

- Nassarawa

- Zamfara

- Sakkwato

- Taraba

Dubi jerin jahohi 14 a Arewacin Najeriya da suka amince a gudanar da sallar Idi
Sallar Idi Hoto: The Defender
Asali: UGC

Amma cibiyar mulki ta Arewacin Najeriya, jahar Kaduna ta sha bambam da takwarorinta game da sassauta dokar, inda jahar ta dauki alwashn dabbaka dokar hana fita a ranar sallah.

Gwamnan jahar, Nasir El-Rufai yace ba zai sassauta dokar bayan samun amincewar malaman jahar Kaduna, don kada nasarar da suka samu a yaki da cutar COVID-19 ya tafi a ranar daya.

Asabar, 23 ga watan Mayu ne ake sa ran gudanar da sallar Idi a Najeriya, idan har an ga watan Shawwal, idan aka samu akasin haka, Sallar Idi zai kama ranar Lahadi, 24 ga watan Mayu.

A wani labari kuma, mai alfarma Sarkin Musulmi ya shawarci Musulman da basu samu daman zuwa Masallaci ba da su gudanar da sallar Idinsu a gida kamar haka;

“Sallar Idi nafila ce mai raka biyu,

“A raka’ar farko ana kabbara guda 7

“Sai a karanta Suratul Fatiha

“Sai a karanta abin da ya sawwaka daga Al-Qur’ani, musamman suratul A’ala

“A raka na biyu kuma kabbara 5 ake yi

“Sai a karanta suratul fatiha

“Sai a karanta abin da ya sawwaka daga Al-Qur’ani, musamman suratul Ghashiyah.

“Amma tun da sallar gida ne, ba lallai sai an yi hudubar bayan Sallah ba.

“Duka wadannan sun tabbata a hadisin Anab bin Malik dake cikin Sahihul Bukhari, da mazhabar Malikiyya, a Mukhtasar ma Al-Kharshi da Al-Munah Al-Jalil sun yi bayaninsa.” Inji shi.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Asali: Legit.ng

Online view pixel