Karamar Sallah: Shugaba Buhari ya bayyana inda zai gudanar da sallar Idin bana

Karamar Sallah: Shugaba Buhari ya bayyana inda zai gudanar da sallar Idin bana

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana cewa a karamar sallar bana, shi da iyalinsa za su gudanar da sallar Idinsu ne a gida.

Fadar shugaban kasa ta bayyana haka ta wata sanarwa da ta fitar ta bakin kakaakin shugaban kasa Malam Garba Shehu a ranar Juma’a, 22 ga watan Mayu a babban birnin tarayya Abuja.

KU KARANTA: Dubi jerin jahohi 14 a Arewacin Najeriya da suka amince a gudanar da sallar Idi

“Buhari ya yanke wannan shawara ne don dabbaka dokar zaman gida da aka sanya a babban birnin tarayya Abuja domin kare rayukan jama’a tare da kare dasu shiga cikin hatsari.

“Haka zalika matakin ya yi daidai da umarnin da mai alfarma Sarkin Musulmai, Alhaji Sa’ad Abubakar ya bayar ta hannun kungiyar Jama’atul Nasril Islam na hana sallar Idi a cikin taron jama’a, da kuma tsarin kwamitin shugaban kasa dake yaki da COVID-19 a Najeriya na hana cunkoson jama’a.” Inji shi.

Karamar Sallah: Shugaba Buhari ya bayyana inda zai gudanar da sallar Idin bana
Buhari da Iyalansa
Asali: Facebook

Bugu da kari, ba kamar yadda saba shugaban kasa yana karbar baki a lokuttan bukukuwan sallah, a wannan karon shugaban ba zai karbi baki ba saboda wadannan dokoki.

Kungiyoyin addini, yan siyasa, manyan jami’an gwamnati, kananan yara, yan uwa da abokan arziki suna kai masa ziyara, amma ya hana a sallar bana don dakile yaduwar coronavirus.

A wani labari kuma, mai alfarma Sarkin Musulmi ya shawarci Musulman da basu samu daman zuwa Masallaci ba da su gudanar da sallar Idinsu a gida kamar haka;

“Sallar Idi nafila ce mai raka biyu,

“A raka’ar farko ana kabbara guda 7

“Sai a karanta Suratul Fatiha

“Sai a karanta abin da ya sawwaka daga Al-Qur’ani, musamman suratul A’ala

“A raka na biyu kuma kabbara 5 ake yi

“Sai a karanta suratul fatiha

“Sai a karanta abin da ya sawwaka daga Al-Qur’ani, musamman suratul Ghashiyah.

“Amma tun da sallar gida ne, ba lallai sai an yi hudubar bayan Sallah ba.

“Duka wadannan sun tabbata a hadisin Anab bin Malik dake cikin Sahihul Bukhari, da mazhabar Malikiyya, a Mukhtasar ma Al-Kharshi da Al-Munah Al-Jalil sun yi bayaninsa.” Inji shi.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Asali: Legit.ng

Online view pixel