Bikin sallah: Ka da mutane su taru su cika wani masallacin idi makil a birane - Sultan

Bikin sallah: Ka da mutane su taru su cika wani masallacin idi makil a birane - Sultan

Majalisar kolin harkokin addinin musulunci a Najeriya ta taya al’ummar musulmai murnar karasowar babbar sallah watau idi da za ayi a karshen makon nan.

NSCIA ta taya daukacin musulman Duniya zagayowar Eid al-Adha, amma kuma ta ja-kunne cewa dole a gujewa yawan cika a filin idi guda a manyan biranen da ke kasar nan.

Jaridar Punch ta fitar da rahoto cewa wannan gargadi da majalisar ta yi ya zo daidai da matakan da hukumomi su ka bada na yaki da annobar cutar Coronavirus a fadin Najeriya.

Majalisar Sarkin musulmin ta kuma yi kira ga musulman kasar da su ka yi niyyar sauke farali, amma ba su samu dama ba, su yi amfani da dukiyar su wajen taimakon al’umma.

Jawabin da Sarkin Musulmin ya yi ya bayyana cewa wadannan ayyukan kyauta da sadaka za su iya jawowa mutum ladar da ta fi ta aikin hajjin da su ka rasa a shekarar nan.

Mai alfarma Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar, ya ce: “Yayin da Eid al-Adha ya ke mana sallama, ya kamata mu kara jaddadawa mutane cewa mu na cikin mawuyacin hali inda abin da ba a saba ba, ya zama abin da aka saba; har da taruwar jama’a da yin sallar jami’i”

KU KARANTA: Sanatan Kano zai kai matasa kasar waje domin su yi kwallo

Bikin sallah: Ka da mutane su taru su cika wani masallacin idi makil a birane - Sultan
Sallar idi a Najeriya Hoto: Gwamnan Kano
Asali: Twitter

Wannan jawabi ya fito ne ta bakin mataimakin sakataren NSCIA, Farfesa Salisu Shehu a ranar Lahadi, 26 ga watan Yuli, 2020.

Muhammad Sa’ad Abubakar ya kara da tunawa jama’a cewa sallar idi ba farilla ba ce, don haka babu dalilin da ya sa sallar ta zama dole idan hakan zai jefa al’umma a hadari.

Farfesa Shehu ya ce shari’ar musulunci ta damu da lafiyar mutane da daukacin al’umma

“Tun da an hana maniyyatan kasashen ketare zuwa aikin hajji a 2020, NSCIA ta na kira ga musulman Najeriya da su ka yi niyya ba su samu dama ba, su yi tunanin amfani da bangaren dukiyarsu (idan ba duka ba) wajen daukar dawainiyar da za ta iya jawo masu ladar aikin hajji ko wanda ta fita.”

A karshen makon nan musulman Duniya za su yi sallar idi, a wannan lokaci kuma mahajjata su na sauke farali a kasa mai tsarki.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel