Bikin Sallah a Kaduna: Na yi wankan sallah amma babu wurin zuwa – Rahama Sadau ta koka

Bikin Sallah a Kaduna: Na yi wankan sallah amma babu wurin zuwa – Rahama Sadau ta koka

Fitacciyar jarumar Kannywood, yar asalin jahar Kaduna, Rahama Sadau ta koka game da dokar tilasta zaman gida a jahar Kaduna da gwamnati ta sanya yayin bikin karamar Sallah.

Gwamnatin Kaduna a karkashin Gwamna Nasir El-Rufai ta sanya dokar hana fita da zirga zirga ne a jahar domin dakile yaduwar annobar Coronavirus mai toshe numfashi.

KU KARANTA: Siyasa mugun wasa: An yi ma wani Kansila zigidir a jahar Zamfara

Don haka daga cikin matakan da gwamnati ta dauka har da dakatar da sallolin jam’I a Masallatai, tun daga sallolin kamsu salawatu, zuwa sallar Juma’ar da kuma sallar Idi.

Wannan tasa jama’an jahar Kaduna basu fita sallar Idi ba, balle kuma yawon sallah a yayin bikin karamar sallar bana, hakan tasa yawancin jama’a daga gida suka yi sallar Idinsu.

Rahama Sadau ta bayyana haka ne a shafin ta na kafar sadarwar zamani na Facebook a ranar Lahadi, inda ta daura kyawawan hotunanta tare da musu taken:

“Wankan Sallah Babu Wurin Zuwa, Barka Da Sallah !! #EidMubarak @ Kaduna”

Sai dai a kafatanin yankin Arewa maso yammacin Najeriya, jahar Kaduna ce kadai ba ta sassauta dokar hana fita ba, sauran jahohi sun janye don baiwa jama’an daman Idi.

Jahohin Katsina, Kano, Jigawa, Zamfara, Sakkwato da Kebbi duk san dage dokar, haka zalika Neja, Nassarawa, Borno, Gombe, Taraba, Adamawa, Bauchi da Yobe, su ma sun janye.

A wani labarin kuma, Hukumar Yaki da Cututtuka Masu Yaduwa a Kasa (NCDC) ta ce annobar cutar Covid-19 ta sake harbin sabbin mutane 313 a fadin Najeriya.

Hakan na kunshe ne a cikin sanarwar da NCDC ta fitar da misalin karfe 11.10 na daren ranar Lahadi, 24 ga watan Mayun na shekarar 2020.

A cikin sanarwar da NCDC ta saba fitarwa a daren kowacce rana a shafinta na Twitter, ta sanar da cewa karin sabbin mutum 313 da suka fito daga jihohin Najeriya.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Asali: Legit.ng

Online view pixel