Masarautar Katsina ta soke shagulgulan babbar sallah

Masarautar Katsina ta soke shagulgulan babbar sallah

- Masarautar Katsina ta yanke hukuncin soke dukkan shagulgulan sallar babba

- An soke shagulgulan sallar ne saboda hauhawar rashin tsaro da kuma annobar korona da ta addabi jihar

- Masarautar ta kuma yi kira ga daukacin Musulmi da su tsananta addu'a a kan Allah ya kawo zaman lafiya a jihar

Masarautar Katsina ta kwaikwayi jihar Kano inda ta yanke hukuncin soke dukkan shagulgulan sallar babba.

A shagalin duk babbar sallah, akwai fitaccen hawan nan da ake kira hawan bariki wanda sarki ke ziyartar gwamnan jihar tare da hawan daba mai kayatarwa.

Wannan na kunshe ne a wata wasika da masarautar ta tura ga sakataren gwamnatin jihar da kuma sa hannun sakataren masarautar Katsina, Mamman Ifo.

Kamar yadda wasikar ta ce, an soke shagulgulan sallar ne saboda hauhawar rashin tsaro da kuma annobar korona da ta addabi jihar.

Amma kuma, masarautar yayin da take taya daukacin Musulmi murna, ta yi kira garesu da su tsananta addu'a a kan Allah ya kawo zaman lafiya a jihar.

Babu takardar da ta bada tabbacin za a yi sallar idi ko ba za a yi ba a fadin jihar a yayin wannan rahoton.

Gwamnatin jihar Katsina ta soke shagulgulan babbar sallah
Gwamnatin jihar Katsina ta soke shagulgulan babbar sallah Hoto: Masarautar Katsina
Source: UGC

Kamar yadda wasikar ta bayyana, "Bayan gaisuwa mai yawa da amana, bayan haka, Mai Martaba Sarkin Katsina, Alhaji Dr Abdulmumin Kabir Usman ya bada umarnin in rubuta wasika don in sanar da ku cewa, bisa ga tashe-tashen hankali da ake samu na 'yan ta'adda wanda yake jawo sanadiyyar rasa rayuka da kuma dumkha, tare da annobar COVID-19.

"Sarkin da 'yan majalisarsa sun zauna tare da yanke shawarar ba za a samu damar gudanar da hawan sallah babba ba.

"Za a taya al'ummar jimamin rashe-rashen da ake samu da kuma kasancewar har yanzu akwai sauran burbushin wannan cutar.

"Don haka zamu ci gaba da addu'o'in na samun zaman lafiya. Allah ya bamu lafiya da zaman lafiya. Ameen," wasikar tace.

A wani labari makamancin haka mun ji cewa gwamnatin jihar Kwara ta soke idin babbar sallar 2020 a fadin jihar.

Gwamnatin tace ta dauki wannan mataki ne bayan hauhawar adadin masu cutar korona a jihar.

Shugaban kwamitin kar ta kwana kan covid 19 na jihar, Kayode Alabi ya bayyana wa manema labarai a birnin Illorin, yace an dauki wannan mataki ne bayan tattaunawa da kungiyar malamai da kuma Sarkin Illorin.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Nigeria

Online view pixel