COVID-19: Jerin jihohin Najeriya 7 da suka haramta bukukuwar Babbar Sallah

COVID-19: Jerin jihohin Najeriya 7 da suka haramta bukukuwar Babbar Sallah

Saboda annobar korona, wasu gwamnatin jihohi sun haramta bukukuwan babbar sallah a lokacin da alummar musulmi ke shirin yin bikin babbar sallah wato Eid-el-Kabir na shekarar 2020.

Ga dai jerin jihohin da suka saka dokokin haramta bukukuwar Sallah a bana domin dakile yaduwar annobar coronavirus kamar yadda Daily Trust ta wallafa.

COVID-19: Jerin jihohin da suka haramta bukukuwar Babbar Sallah
COVID-19: Jerin jihohin da suka haramta bukukuwar Babbar Sallah. Hoto daga BBC Pidigin
Asali: Twitter

1. Jihar Kano

Gwamnatin Jihar Kano ta sanar da soke bukukuwar babbar sallah a jihar.

Gwamnatin ta yi bayanin cewa ta dauki wannan matakin ne domin cigaba da dakile yaduwar cutar korona a jihar musamman idan anyi laakari da cewa an sasautar dokar kulle.

Amma an bawa mutane damar fita su tafi masallatai suyi sallar Idi duk da cewa an gindaya sharruda na kiyaye yaduwar cutar a jihar.

2. Jihar Plateau

Rundunar yan sandan jihar Filato ta ce ba za ayi sallar Idi a masallatan Idi a jihar ba yayin sallar shekarar 2020.

Sanarwar yan sandan ta ce za a iya yin sallar ta Idi a masallatan yankin Arewa amma kada mutane su wuce hamsin a masallatan kamar yadda dokar hana yaduwar cutar korona ta jihar ta tanada.

An kuma sanar da rufe dukkan wuraren shakatawa a jihar na tsawon mako guda daga yau Juma'a 31 ga watan Yuli.

3. Birnin Tarayya Abuja

Ministan babban birnin tarayya Abuja, FCT, Muhammad Musa Bello shima ya ce ba za a bari ayi sallar Idi a masallatai ba.

Ministan ya kuma ce ba za a yi sallar Idi a babban masallacin kasa da ke birnin tarayyar ba kuma kada sallar ta wuce awa guda a wuraren da aka bari ayi.

Ya kuma kara da cewa mutane su yi duk wani bukin sallar a gidajensu.

4. Jihar Osun

Gwamnatin jihar Osun ta ce ta soke bukukuwan babbar sallah a jihar.

Sakataren gwamnatin jihar, Wole Oyebamiji ya ce ba za ayi sallar Idi ba saboda annobar korona. Ya ce za ayi sallar Juma'a bisa kiyaye dokokin yaduwar annobar.

DUBA WANNAN: Illolin karas 5 ga jikin ɗan adam da ba kowa ya sani ba

5. Jihar Niger

Gwamna Abubakar Sani Bello na jihar Niger ya soke dukkan bukukuwan babbar sallah a masarautu takwas na jihar.

Amma gwamnan ya bayar da izinin ayi sallar jam'i a masallatan Juma'a a jihar shima bisa bin dokokin kiyaye yaduwar cutar korona.

6. Jihar Kwara

Gwamnatin jihar Kwara ita ma ta soke bukukuwan na babbar sallah.

Mataimakin gwamnan kuma shugaban kwamitin yaki da korona, Kayode Alabi ya ce daukan matakin ya zama dole duba da yawan mutanen da ake sa ran za su taro yayin sallar idin da yiwuwar yaduwar cutar.

Ya ce za ayi sallar Juma'a a jihar amma za a rika bayar da tazara da amfani da takunkumin fuska.

7. Jihar Jigawa

Gwamnatin jihar Jigawa ita ce ta soke bukukuwan sallah a jihar. Sai dai gwamnatin ta ce mutane suna iya zuwa filayen Idi su gudanar da sallolin su.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel