Atiku ko Tinubu: An Raba Gardama kan Dan Takarar da Ya Fi Dacewa da Mulkin Najeriya
- Dele Momodu ya ce Atiku Abubakar ne ɗan takarar da ya fi dacewa da shugabancin Najeriya a zaɓen 2027
- Momodu ya kwatanta tarihin siyasar Atiku, Bola Tinubu da Peter Obi, bisa mukaman da kowannensu ya riƙe a baya
- Jigon na ADC ya yi zargin cewa Tinubu ya yi kuskuren ɗaukar Najeriya tamkar Legas ne lokacin da ya zama shugaban ƙasa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Dele Momodu, Mataimakin Darakta-Janar mai kula da yaɗa labarai da sadarwa na kwamitin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na jam’iyyar ADC, ya yi magana kan Atiku Abubakar.
Dele Momodu ya bayyana ɗan takarar jam’iyyar, Atiku Abubakar, a matsayin wanda ya fi dacewa da zama shugaban kasa a zaɓen 2027.

Source: Facebook
Momodu ya bayyana hakan ne yayin wata hira da aka yi da shi a shirin Politics Today na tashar Channels Tv a ranar Alhamis, 22 ga watan Oktoban 2026.
Ya ce tun lokacin da Atiku ya fara neman shugabancin Najeriya a shekarar 1993, ya kasance ɗan takarar da ya fi nuna tsari, mayar da hankali da ƙudurin cimma burinsa na zama shugaban ƙasa.
Jigon ADC ɗin ya kuma yi iƙirarin cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu, wanda ke neman wa’adi na biyu a ƙarƙashin jam’iyyar All Progressives Congress (APC), ya san cewa Atiku ya fi dacewa da wannan muƙami.
Momodu ya ce Tinubu ya san ƙwarewar Atiku
Da yake bayyana dalilin da ya sa yake ganin Atiku ne mafi dacewa, Momodu ya ce ra’ayinsa ya dogara ne da tarihin siyasa da ƙwarewar tsohon mataimakin shugaban ƙasar.
“Lokacin da na ce shi (Atiku) ne mafi dacewa, magana ce ta gaskiya, kuma hatta Shugaba Bola Tinubu da kansa ya san hakan.” In ji shi.
Momodu ya ƙara da cewa akwai lokacin da Tinubu ya gayyaci Atiku, suka haɗa kai domin Atiku ya tsaya takarar shugaban ƙasa a baya.
Ya kwatanta Tinubu, Atiku da Peter Obi
Momodu ya kwatanta ƙwarewar manyan ‘yan takarar shugaban ƙasa uku da ake magana a kansu, wato Bola Tinubu na APC, Atiku Abubakar na ADC da Peter Obi na Nigeria Democratic Congress (NDC).
A cewarsa, babban abin da Tinubu zai iya nunawa a tarihin aikinsa shi ne kasancewarsa tsohon gwamnan Jihar Legas.
Ya bayyana cewa mafi girman ƙwarewar Atiku ita ce gogewarsa a matsayin tsohon mataimakin shugaban ƙasar Najeriya, yayin da ta Peter Obi ita ce kasancewarsa tsohon gwamnan Jihar Anambra.
Momodu ya ce idan aka yi la’akari da waɗannan mukamai, masu zaɓe za su iya tantance bambancin ƙwarewar ‘yan takarar uku.
Ya zargi Tinubu da kuskuren fahimtar Najeriya
Momodu ya kuma soki yadda Tinubu ke tafiyar da mulkin ƙasar, inda ya yi zargin cewa shugaban ya yi kuskuren ɗaukar Najeriya tamkar Jihar Legas ne lokacin da ya hau kujerar shugaban ƙasa.
A cewarsa, shugabancin Legas ya bambanta da jagorantar Najeriya baki ɗaya, saboda bambancin yanayi da ƙalubalen da ake fuskanta a ƙasar.
Ya ce Tinubu ya fahimci cewa Najeriya ta bambanta da Legas ne bayan ya zama shugaban ƙasa, kuma hakan ya jawo abin da ya kira babban rudani a tafiyar da mulkinsa.

Source: Twitter
Atiku ba zai iya kifar da Tinubu ba
A wani labarin kuma, kun ji cewa Dr Musa Iliyasu Kwankwaso, ya yi magana kan tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar.
Musa Iliyasu Kwankwaso ya ce Atiku ba shi da tasirin siyasa da goyon bayan Arewa irin na marigayi Shugaba Muhammadu Buhari da zai iya barazana ga ƙoƙarin Shugaba Bola Tinubu na sake lashe zaɓen 2027.
Asali: Legit.ng


