Dokar hana fita na nan a Kaduna, babu gudu babu ja da baya – Gwamnati

Dokar hana fita na nan a Kaduna, babu gudu babu ja da baya – Gwamnati

Gwamnatin jahar Kaduna ta tabbatar da dokar hana fita a jahar Kaduna, sa’annan ta dauki alwashin tabbatar da dokar hatta a ranar karamar Sallah na bana.

Gwamnatin ta sanar da haka ne bayan taron majalisar tsaro daya gudanar a ranar Alhamis a fadar gwamnatin jahar inda ta bayyana Laraba da Alhamis a matsayin ranakun fita kawai.

KU KARANTA: Sarkin Musulmi ya yi bayani game da yadda ake Sallar Idin mutum 1 a gida

Kwamishinan tsaro na jahar Kaduna, Samuel Aruwan ne ya bayyana haka cikin wata sanarwa da ya fitar, inda yace an baiwa hukumomin tsaro daman dabbaka dokar a sauran ranaku.

Don haka ake kira ga jama’a su bi dokokin da aka tsara, da suka hada da hana tafiye tafiye, hana duk wani taron ibada da kuma hana tarukan biki, ko na siyasa ko kuma na wani hidima.

Dokar hana fita na nan a Kaduna, babu gudu babu ja da baya – Gwamnati
Dokar hana fita
Source: UGC

Gwamnatin ta ce dalilinta da na daukan wannan mataki shi ne don kare rayukan al’umma, don haka ake rokon jama’a su yi hakuri da halin da ake ciki domin kare kansu da kowa da kowa.

“A kokarinmu na tabbatar da bin doka da oda, jami’an tsaro za su kara kaimi wajen gudanar da sintiri, haka zalika za’a karfafa matakan tsaro game da hana shige da fice a jahar tun daga bakin iyakar jahar.

“Jami’an tsaro za su kasance masu nuna ya kamata da kwarewa wajen aikinsu, ana iya sanar da mu duk wani cin zarafi na jami’an tsaro a lan lambobin 09034000060 da 08170189999.” Inji shi.

Daga karshe Aruwan ya ce gwamnatin na kira ga jama’a su kasance cikin zaman lafiya kuma su baiwa hukumomin tsaro hadin kai wajen gudanar da ayyukansu.

A wani labari, incike na tsimi da tanadi da hukumar kiddiga ta Najeriya ta gudanar ya nuna tattalin arzikin Najeriya zai shiga halin tabarbarewa da kashi -4.4 saboda annobar Coronavirus.

Premium Times ta ruwaito ministar kudi, Zainab Ahmad ce ta bayyana haka ga manema labaru bayan kammala taron majalisar tattalin arzikin kasa daya gudana a ranar Alhamis.

“Hukumar kididdig ta gudanar da bincike, kuma sakamakon binciken ya nuna tattalin arzikin Najeriya za ta shiga mawuyacin hali, za ta fadi da kashi -4.4, amma duba da aikin da kwamitin tayar da komar tattalin arzikin kasa take yi, muna sa ran zamu rage radadin faduwar tattalin arzikin.” Inji ta.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Source: Legit.ng

Online view pixel