Allah ya karbi ibadan azumin da ku ka yi – Jonathan ga Musulmai

Allah ya karbi ibadan azumin da ku ka yi – Jonathan ga Musulmai

- Goodluck Jonathan ya aikawa Musulmai sakon barka da Sallah jiya

- Tsohon Shugaban ya tuna da al’ummar Musulmai a lokacin bikin idi

- Jonathan ya yi wa Musulmai addu’ar Allah ya karbi taron ibadunsu

Yayin da ake yin bikin karamar sallah a fadin Duniya, tsohon shugaban Najeriya, Dr. Goodluck Jonathan ya taya Musulmai murnar wannan rana mai daraja.

Tsohon shugaban kasar ya aikawa al’ummar Musulmai sakon farin cikin sallar ne a shafinsa na tuwita. Ya yi wa musulman addu’ar a karbi ibadun da su ka yi.

Dr. Goodluck Jonathan wanda ya mikawa Muhammadu Buhari mulki ya ce: “Ina taya al’ummar Musulmai murna a wannan ranar karamar sallah ta farin ciki.”

Jonathan ya kara da cewa: “Ina addu’a ga Allah ya cigaba da sauko da falalarsa a gidajenku, ya kuma lullube kasarmu da falalarsa.”

KU KARANTA: Muhammadu Sanusi II ya yi sallar idin farko bayan barin gidan dabo

“Allah Madaukakin Sarki ya karbi dukkanin ibadunku, ya kuma ba ku lada.” inji Jonathan.

Har ila yau, Jonathan bai tsaya nan ba, ya kara da cewa: “Allah ya kawo maku aminci da zaman lafiya.”

A karshe ya rubuta: “Barka Da Sallah.”

Shugaba Goodluck Jonathan ya yi sammakon aika wannan sako ne a jiya Ranar 24 ga watan Mayu, 2020 da karfe 6:44 na safe (a agogon Najeriya).

Kawo yanzu kusan mutane 1000 sun yada wannan sako, bayan haka akwai mutane fiye da 7000 da su ka nuna cewa sakon tsohon shugaban ya burge su.

Jonathan ya mulki Najeriya na tsawon shekaru biyar tsakanin 2010 zuwa 2015. Shugaban ya sauka daga gadon mulki ne bayan ya rasa tazarce a 2015.

Manyan kasar da-dama irinsu Atiku Abubakar, Bukola Saraki sun taya al’ummar Musulmai murnar ganin karshen watan azumi da zuwan karamar idi.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel