'Yan Sanda Sun Gargadi 'Yan Siyasar Kwara Kan Taron Siyasa a Filin Sallar Idi

'Yan Sanda Sun Gargadi 'Yan Siyasar Kwara Kan Taron Siyasa a Filin Sallar Idi

- Rundunar 'yan sanda a jihar Kwara ta gargadi 'yan siyasa kan gudanar da tarukan siyasa a filin Idi

- Haka nan an shawarci mazauna yankin da su kula sosai wajen gudanar da bukukuwan karamar sallah

- Hakazalika rundunar ta bada lambobin waya don ba da rahoton duk wani wanda ake zargi a yankin

Rundunar ‘yan sanda ta Kwara ta gargadi 'yan siyasa a jihar kan amfani da filin Sallar Idi wajen tarukan siyasa, The Cable ta ruwaito.

Kamfanin dillacin labarai na Najeriya (NAN) ya ruwaito cewa, Mohammed Bagega, kwamishinan ‘yan sanda na jihar, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da Ajayi Okasanmi, kakakin rundunar 'yan sandan jihar ya fitar a ranar Talata

Ya ce wasu mutane na shirin hargitsa Sallar Idi don haka, ya gargadi mazauna yankin kan gudanar da tarukan siyasa a wurin da ake gudanar da Sallar.

KU KARANTA: Yunkurin Fashi a Fadar Shugaban Kasa Ya Nuna Buhari Ba Zai Iya Tsare Najeriya ba, PDP

'Yan Sanda Sun Gargadi 'Yan Siyasar Kwara Kan Taron Siyasa a Filin Sallar Idi
'Yan Sanda Sun Gargadi 'Yan Siyasar Kwara Kan Taron Siyasa a Filin Sallar Idi Hoto: dailytrust.com
Asali: Depositphotos

Bagega ya ce duk wanda aka kama da makami za a dauke shi a matsayin mai laifi, ya kara da cewa rundunar 'yan sanda ta kuduri aniyar daukar matakin hukunta duk wanda aka samu yana aikata laifi kafin, da kuma bayan bukukuwan sallah.

"Ina so in yi amfani da wannan kafar sadarwa don sanar da mutanen Kwara cewa wasu mutane sun kammala shirye-shirye don tarwatsa zaman lafiya da daidaito a cikin jihar ta amfani da filin Sallar Idi a matsayin wurin taro," in ji shi.

“Don haka, rundunar ta gargadi 'yan siyasa da kada su juya filin sallar Idi zuwa na taron siyasa. Duk wanda aka samu da wasu abubuwa masu hadari kamar makamai da alburusai za a dauke shi a matsayin mai laifi.

“Ba a yarda da ruwan leda a filin sallah ba kasancewar an samar da wadataccen ruwa don alwala.

“Ba za a yarda da rera taken jam’iyya ko wane iri ba, ba za a yarda a rera wakar yaba manyan mutane a cikin filin sallar ba.

"An shawarci masu ababen hawa da su mutunta 'yancin sauran masu amfani da titin saboda duk wani aiki na rashin da'a zai fuskanci hukunci mai tsauri."

Kwamishinan 'yan sanda, ya tabbatarwa da mazauna yin biki ba tare da tashin hankali ba, yana mai cewa an shirya tsaf domin samar da tsaro.

Ya taya Musulmai murnar kammala azumin Ramadana cikin nasara kuma ya bukace su da su more hutunsu ba tare da wata fargaba ba.

Ya kuma shawarci jama'a da su kai rahoton wadanda ba su yarda da su ba ta hanyar amfani da wadannan lambobi: 08126275046 da 07032069501.

KU KARANTA: Jerin Kasashen Da Basu Ga Wata Ba, Ba Kuma Za Su Yi Sallar Idi Gobe Laraba Ba

A wani labarin, Kwamitin Sarkin Musulmi kan harkokin addini tare da hadin gwiwar Kwamitin Duban Wata a Najeriya sun sanar da cewa ba su samu labarin ganin watan Shawwal a Najeriya ba a yau Talata 11 ga watan Mayun wanda ya yi dai-dai da 29 ga watan Ramadana.

Don haka Sarkin Musulmi, Sultan Muhammad Sa'ad Abubakar CFR, ya ayyana Alhamis 13 ga watan Mayu 2021 a matsayin ranar Sallah kuma 1 ga watan Shawwal.

Sarkin Musulmi ya taya Musulmin Najeriya murna tare da fatan Allah ya yi masu albarka.

Asali: Legit.ng

Online view pixel