Jama’a Sun Ji Haushin Sanusi II da Sarkin Ya Kawo Shawarar Gyara Tattalin Arziki

Jama’a Sun Ji Haushin Sanusi II da Sarkin Ya Kawo Shawarar Gyara Tattalin Arziki

  • Khalifa Muhammadu Sanusi II ya ja kunnen Gwamnatin Najeriya game da shigo da tsarin kawo abinci daga waje
  • Sarkin Kano ya ce bude kasuwa a kawo kayan abincin kasashen ketare ya kashe kamfanonin da suke nan gida
  • Masanin tattalin arzikin kuma tsohon gwamnan babban bankin Najeriya ya danganta hakan da karuwar bashi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada

Kano - Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II ya sake nuna goyon bayansa ga rufe iyakoki domin hana shigo da abinci.

Ta fuskar tattalin arziki, Mai martaba Muhammadu Sanusi II yana ganin wannan tsari zai taimaka wa Najeriya.

Sarkin Kano
Sarkin Kano, Muhammad Sanusi II yana magana a Afrika ta Kudu Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Gargadin Muhammadu Sanusi II ga gwamnati

Tashar TRT Afrika ta rahoto Sarkin Kano yana gargadin Gwamnatin tarayya ta guji bada dama a shigo da abin da za a ci.

Khalifa Sanusi II yana da ra’ayin cewa kawo shinkafa daga Thailand da sauran kasashen waje ba alheri ba ne ga kasar nan.

Kara karanta wannan

Tinubu: Nasir El Rufai ya daura bidiyon abin da Sarkin Katsina ya fada wa Abdulaziz Yari

Jagoran na Tijjaniya yake cewa a sanadiyyar haka, an durkusar da kamfanonin da ke casar shinkafa.

Wannan kuma zai jawo matasa da ke aiki a kamfanonin su rasa aikin yi, sannan zai taba dinbin manoma da ke karkara.

Tsohon gwamnan na bankin CBN ya ce kamfanonin nan sun ci bashin banki da a yanzu sun gagara biya saboda hakan.

Sanusi II ya kushe tsarin ne da yake bayani wajen wani taro da aka shirya a Legas dangane da yadda za a kawo cigaba.

A mazhabar masanin tattalin arzikin, kyau Najeriya ta dogara ne da abin da za ta ci maimakon ta rika jiran kasashen waje.

Mutane sun yi tir da Muhammadu Sanusi II

Amma da alama mutanen da suka bibiyi labarin ba su ji dadin wannan kira ba, suna ganin muguwar shawara sarkin ya bada.

Jama’a da-dama sun koka cewa a dalilin hana shigo da shinkafa domin karfafa ‘yan kasuwan gida ne abinci ya gagari talaka.

Wasu ba su damu ba ko manoma a Najeriya za su kare idan dai za su ci abinci da araha.

Kara karanta wannan

Akwai yiwuwar ma’aikata su shiga yajin aiki, ba a dace a zaman da aka yi da gwamnati ba

"Rashin shigo da shinkafar kuma ta durkusar da Al'umma gaba ɗaya, wasu ma sun mutu saboda yunwa."

- Muhammad Shariff

Sufyanu Rabe Danladi ya ce:

"Malam Sanusi wani lokacin Shawarar ka bala'i take jefa yan Nigeria (ku ne gaba-gaba wajen bada shawarar a cire tallafi)"

Shi Mustapha Abubakar tambayi ya yi:

"Ranka ya daɗe, ka fi son masu shinkafar ta gida su ci gaba da azabtar da talakawa saboda kai baka sayen ta ko?

Ya cigaba:

"To in dai talakawa za su samu sauƙin awo a shinkafar wajen, Allah ya durƙusar da kamfanonin gida har abada kar su tashi."

Bappaji Sulaiman Nafada ya ce:

"Cikin girmamawa Kamfanonin su cigaba da durkucewa tun da dai talaka yana samun sa'ida"

Wani bakano kuwa cewa ya yi yana kaunar Sanusi II, amma saboda irin shawarwar yake goyon bayan Aminu Ado.

Umar Muhammad ya ke tambaya:

“So yake yunwa ta kashe mu?”

Malam Abdulhayatu Sama'ila Misku yake cewa:

"Gaskiya shawararka wani lokacin talaka ba ya ganin amfanin ta."

Wasu tsiraru suna tare da Sanusi II

Kara karanta wannan

Tinubu ya sake bude hanyar Kano zuwa Zariya da Marigayi Buhari ya bude tun 2023

Daidaikun mutane suka yi maraba da maganar Mai martaba, wasu kuma sun ce noma ya kara wahala saboda rashin tsaro.

Ameer Lukman Haruna wanda ma’aikacin banki ne da ya fahimci tattali, ya goyi bayan sarkin, ya rubuta illar kawo abinci daga waje.

“Ba ma maganar dubban ayyukan yi da mutane suka rasa ba, lamarin da ya ƙara tsananta rashin aikin yi da talauci, tare da jefa ma’aikatan da abin ya shafa cikin wahala.
Haka kuma, hakan ya rage masu sha’awar zuba jari na cikin gida da na ƙasashen waje, sakamakon rashin tabbas da ke tattare da saka jari da yanayin kasuwanci a Najeriya. Ga kuma (lamarin isasshen abinci), duk randa wani abu ya faru aka kulle mashiga sai an ji jiki.
Allah ya kyauta”

Sarkin Katsina ya yi wa 'yan APC kashedi

An ji labarin yadda Sarkin Katsina ya fada wa masu tallar Bola Ahmed Tinubu maganganun da za su yi masu daci da suka je fadar shi.

Da alama Malam Nasir El-Rufai wanda a yanzu yana hannun hukuma ya ji dadin abin da ya faru a Katsina, har ya daura a shafukansa.

Abdulmumin Kabir Usman ya nuna wa Abdulaziz Yari bai jin ganin dadin bita-da-kulli, rashin tsaro da wasu matsalolin da Arewa ke ciki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng